Jonathan ya jagoranci babban gangamin Atiku a Sokoto

Jonathan ya jagoranci babban gangamin Atiku a Sokoto

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da wasu manyan mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sun bi sahun dubban masoya a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba, a Sokoto don kaddamar da kamfen din arewa maso yamma na dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa da farko Atiku ya shirya zuwa Sokoto don halartan gangamin da rana, amma ya isa birnin da karfe 2pm sannan kai tsaye ya tafi Kangiwa square tare da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Wadanda suka yiwa dan takarar rakiya sune jami’an jam’iyyar daga jihohin arewa maso yamma bakwai wadanda suka hada da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Jigawa, Katsina, Kano da kuma Kaduna.

KU KARATA KUMA: Yanzu Yanzu: Ya majalisa 26 sun sauya sheka daga APC zuwa APM a Ogun

Shugaban jam’iyyar, Uche Secondus yayi jawabi ga tarin magoya baya inda ya bukaci da su yi waje da gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel