Zaben 2019: Atiku ya gana da Wike gabannin fara kamfen

Zaben 2019: Atiku ya gana da Wike gabannin fara kamfen

Gabannin bude kamfen dinsa a yau, Litinin, 3 ga watan Disamba, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party( PDP) Atiku Abubakar, ya gana da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, wanda ya yi murabus daga matsayin shugaban kamfen dinsa a kudu maso kudu a jiya.

Atiku ya roki Wike, inda ya ba gwamnan tabbacin cewa daga yanzu za’a sanya shi cikin manyan masu yake shawara akan kamfen din.

Zabe 2019: Atiku ya gana da Wike gabannin fara kamfen

Zabe 2019: Atiku ya gana da Wike gabannin fara kamfen
Source: UGC

Gwamnan ya bayyana cewa shi baida wani manufa akan Atiku amma cewa shugabancin PDP na kokarin mayar da shi saniyar ware.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ya majalisa 26 sun sauya sheka daga APC zuwa APM a Ogun

Ana ganin Wike na iya janye kudirinsa na yinmurabus daga shugaban kula da kamfen din kudu-maso-kudu.

Sannan kuma Atiku na iya sasanta shugaban jam’iyyar da Wike kan korafin da gwamnan yayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel