Yemi Osinbajo yayi wata muhimmiyar ganawa da Yari, Kashim da El-Rufai

Yemi Osinbajo yayi wata muhimmiyar ganawa da Yari, Kashim da El-Rufai

Labarai sun iso mana daga fadar Shugaban kasa yanzu haka cewa Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari yana tare da Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo inda su ke wata ganawa mai muhimmanci.

Yemi Osinbajo yana wata muhimmiyar ganawa da Gwamnan Zamfara Yari

Yari yana ganawa da Farfesa Osinbajo a cikin fadar Aso Villa
Source: Facebook

Gwamna Abdulaziz Yari wanda shi ne Shugaban Gwamnonin Najeriya ya isa fadar Shugaban kasar na Aso Villa dazu da rana tsaka ne inda bai tsaya ko ina ba sai ofishin Mataimakin Shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo.

Kamar yadda labari ya zo mana, Gwamna Abdulaziz Yari ya iso fadar na Aso Villa da ke babban Birnin Tarayya Abuja da kimanin karfe 2:00 na rana ne. Har yanzu dai Gwamnan na Jam’iyyar APC bai fito daga fadar Shugaban kasar ba.

KU KARANTA: Saraki ya fara sabon lissafi a bayan APC ta sha kasa a zaben Kwara

Haka kuma babu wanda ya san wace wainar ake toyawa tsakanin babban Gwamnan da kuma Mataimakin Shugaban kasar. Sai dai babu mamaki tattaunawar ba ta rasa nasaba da rigimar da ya barke a Jam’iyyar APC mai mulkin Kasar.

Abdulaziz Yari yana cikin Gwamnonin da ke sa-in-sa da Shugaban Jam’iyyar APC watau Adams Oshiomhole. Kwanaki dai aka ji Gwamna Yari yana yi wa Shugaban na APC barazana game da zaben fitar da gwani na Gwamna a Jihar sa.

Sauran wadanda su ke takaddama da Shugaban APC na kasa su ne Gwamna Rochas Okorocha na Jihar Imo da kuma Ibikunle Amosun. Yanzu haka dai Gwamnonin Jam’iyyar biyu sun fara nuna alamun tuburewa APC a babban zaben 2019.

KU KARANTA: 2019: Atiku ya dinke barakar sa da Inyamuran Jam’iyyar PDP

Labari ya kara zuwa mana baya cewa Mataimakin Shugaban kasar ya kuma gana da wasu Gwamnonin na APC a zaman. Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai da kuma Gwamna Kashim Shettima sun halarci wannan taro da aka yi.

Haka kuma Ministar kudi Zainab Ahmed ta halarci wannan kus-kus da aka yi a fadar Shugaban kasa tare da Gwamnonin nan Jihar Borno da kuma Kaduna da Zamfara. Har yanzu dai babu wanda ya san abin da aka tattauna a kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel