Atiku da Buhari za su iya faduwa zaben 2019 - Faston da ya yi hasashen nasarar Buhari a 2015

Atiku da Buhari za su iya faduwa zaben 2019 - Faston da ya yi hasashen nasarar Buhari a 2015

- Rabaran Fada Ejike Mbaka ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar Shugaba Buhari da Atiku Abubakar su sha kaye a zaben 2019

- Ya kuma ce addu'o'in da cocinsa ta rika yiwa Buhari a shekarar 2015 na ya warkar da shi daga rashin lafiyar da ya yi fama da ita

- Mbaka ya kara da cewa har yanzu Shugaban kasar bai yiwa cocinsa komai ba domin nuna godiyarsa ga Ubangiji

Limamin darikar Kotolika kuma shugaban Adoration Catholic Prayer Ministry da ke Enugu, Reverend Father Ejike Mbaka ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar Shugaba Muhammadu Buhari da dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar za su fadi sha kaye a zaben 2019.

Babban malamin addinin ya fadi hakan ne a yayin bikin baje kolin amfanin gona na 2018 a Adoration Ground da ke garin Emene.

Atiku da Buhari za su iya faduwa zaben shekarar 2019 - Faston da ya yi hasashen nasarar Buhari a 2015

Atiku da Buhari za su iya faduwa zaben shekarar 2019 - Faston da ya yi hasashen nasarar Buhari a 2015
Source: Twitter

Ya yi ikirarin cewa adduo'in da 'yan cocin adoration su kayi ne ya sanya Buhari samun nasarar zama shugaban kasa. Mbaka ya koka kan yadda shugaban kasar ya ki zuwa cocin ya yi wani aiki ko bayar da gudunmawa domin nuna godiyarsa ga Allah.

DUBA WANNAN: Za mu sake dawowa: Fusatattun 'yan fashi sun aika takarda gidajen jama'ar da su ka gudu

Ya kuma yi ikirarin cewa addu'o'in mabiya cocinsa ne ya warkar da shugba Buhari daga rashin lafiyar da ta same shi a shekarar 2015.

Vanguard ta ruwaito Mbaka ya ce: "Ku tambayi Atiku idan yana tunanin irin wannan tattakin ne shanu zai yi har ya tafi Umuahia." Ya kammala jawabinsa da cewa Atiku ya garzaya ta ziyarci cocinsa na da ke Adoration groundya basu gudunmawa kamar yadda Ike Ekweremadu ya yi.

Limamin cocin ya cacaki abokin takarar Atiku, Peter Obi. Ya ce babu abinda Obi ya yiwa cocinsa.

"Umahi ya bamu gudunmawa buhunnan shinkafa 1,000 da doya 1,000 amma wannan bai girgiza ni ba sai da ya mika min Cheque na zunzurutun kudi Naira miliyan 10 kuma ya yi alkawarin zai gina mana sabuwar coci. Wannan shine irin gudunmawar da muke bukata daga Obi," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel