Kada ka sanya hannu a sabon dokar zabe kafin 2019 – Yan takarar shugaban kasa sun gargadi Buhari

Kada ka sanya hannu a sabon dokar zabe kafin 2019 – Yan takarar shugaban kasa sun gargadi Buhari

Kungiyar yan takarar kujeran shugaban kasa sun gargadi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan sanya hannu a sabon dokar zabe da aka yiwa gyara wacce majalisar dokokin kasar suka gabatar masa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar ta soki sashin sabon dokar, wanda ya bukaci tantance masu zabe da na’ura da kuma watsa sakamako.

Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kungiyar kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Advanced Peoples Democratic Alliance (APDA), Alhaji Shitu Mohammed Kabir, ya bayyana cewa sabon dokar zaben na cike da ababen da ka iya kawo cikas a zaben 2019.

Kada ka sanya hannu a sabon dokar zabe kafin 2019 – Yan takarar shugaban kasa sun gargadi Buhari

Kada ka sanya hannu a sabon dokar zabe kafin 2019 – Yan takarar shugaban kasa sun gargadi Buhari
Source: Depositphotos

Dan takarar shugaban kasar na APDA ya yi barazanar maka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a kotu idan har suka gabatar da dokar.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi namijin kokari, ya cancanci yin tazarce – Abdullahi Adamu

Kabir, wanda yayi magana bayan taron yan takarar shugaban kasa 40 wanda aka yi a karshen mako, yayi muhawarar cewa INEC ba ta da karfin magance matsalolin da ka iya tasowa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel