Atiku ya lallabi jiga-jigan PDP na Kudancin Najeriya da su zo a hada-kai

Atiku ya lallabi jiga-jigan PDP na Kudancin Najeriya da su zo a hada-kai

‘Dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar yana kokarin lallabar wadanda su ka fusata a Jam’iyyar a dalilin daukar Pater Obi da yayi a matsayin Abokin takarar sa.

Atiku ya lallabi jiga-jigan PDP na Kudancin Najeriya da su zo a hada-kai

'Dan takarar Shugaban kasa Atiku ya shawo kan 'Yan PDP da ke Kudunacin Najeriya
Source: Depositphotos

Wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP a Kasar Inyamurai ba su ji dadin yadda Atiku Abubakar ya zabi Peter Obi a matsayin ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa ba tare da ya tuntube su ba, wasu ma dai su na harin samun wannan matsayi.

Daga cikin wadanda su ka nuna fushin su akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu. Babban Sanatan ya ci burin cewa Atiku zai zabe sa a matsayin Abokin takaran na sa a zaben 2019 amma ba haka aka yi ba.

KU KARANTA: Yadda zan bi wajen maganin ‘Yan Boko Haram – Atiku Abubakar

Atiku yayi kokarin shawo kan manyan PDP da su ka nuna fushin su a kan wannan mataki inda ya ziyarci kusoshin Jam’iyyar da ke Yankin Kudu maso Gabas. Daily Trust ta rahoto cewa yanzu Atiku ya sasanta da ‘Yan PDP a Yankin.

A wancan makon ne dai aka dage babban taron NEC na PDP zuwa Ranar Alhamis, wannan ya bada dama Atiku ya lallabi wadanda su ke ganin ba ayi masu daidai ba. Daga cikin wadanda su ka halarcin taron har da Ike Ekweremadu.

Cif Sam Nkire wanda yana cikin manyan Jam’iyyar ya tabbatar da cewa komai ya lafa a halin yanzu a Jam’iyyar. Yanzu haka dai Atiku Abubakar ya gana da Gwamnan Ribas Nyeson Wike kafin ya soma yawon yakin neman zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel