Shehu Sani ya kalubalanci Buhari da bayyana wadanda suka so aikin Osinbajo

Shehu Sani ya kalubalanci Buhari da bayyana wadanda suka so aikin Osinbajo

Sanata Shehu Sani ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan ya ambaci sunayen wadanda suka nemi Yemi Osinbajo ya nada su a matsayin mataimakin shugaban kasa a lokacin das hi Buhari) ke jinyar rashin lafiya.

Sani wanda ke martani ga ikirarin shugaba Buhari na cewa wasu mutane sun zata ya mutu ne a lokacin da yake jinya a 2017, ya ce yana tsoron kan idan ba’a bayyana sunayen makisan ba yanzu sai yan Najeriya sun tsaya jiran tsammani na tsawon shekaru kafin a gano mutanen a littafin shugaban kasar.

Sanatan mai wakilta Kaduna ta tsakiya yayi wannan kiran ne a ranar Litin, 3 ga watan Disamba a shafinsa na twitter.

Shehu Sani ya kalubalanci Buhari da bayyana wadanda suka so aikin Osinbajo

Shehu Sani ya kalubalanci Buhari da bayyana wadanda suka so aikin Osinbajo
Source: Depositphotos

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu ya fasa kwan da jama'a suka dade suna tattali. Da dadewa, jita-jita ya yadu cewa wasu mutane da ya hada da wani gwamnan Arewacin Najeriya kamar yadda aka yada ya so Buhari ya mutu domin a bashi kujeran mataimakin shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Dansadau ya fara kamfen, ya sha alwashin kawo karshen fashin shanu a Zamfara

A ranar Lahadi, 2 ga watan Disamba 2018, Buhari ya bayyana cewa yayinda yake jinya a Ingija, wasu sun garzaya wajen mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, domin neman kujeransa tunda Buhari ya mutu.

Yace: "Ko Farfesa Osinbajo ya fuskanci wadannan jita-jita - Wasu sun sameshi domin ya zabesu matsayin mataimakan shugaban kasa saboda suna tunanin cewa na mutu. Wannan abu ya fusatashi sosai; kuma ya laburta mini lokacin da ya ziyarceni ina jinya."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel