Najeriya ta datse shigo da kayan abinci, ta tara $21bn a watanni 34 - Emefiele

Najeriya ta datse shigo da kayan abinci, ta tara $21bn a watanni 34 - Emefiele

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa lissafin kudin abincin da ake shigowa da shi Najeriya duk wata ya sauka daga $665.4m a watan Janairun 2015 zuwa $160.4m a watan Oktoba 2018.

Ya ce ragin shigo da kayayyakin abinci sun kama daga shinkafa, kifi, madara, siga da kuma alkama, inda ya kara da cewar za’a ci gaba akan haka.

Emefiele ya bayyana hakan ne a wajen taro cin abinci na ma’aikatan bankuna a jihar Lagas.

Najeriya ta datse shigo da kayan ainci, ta tara $21bn a watanni 34 - Emefiele

Najeriya ta datse shigo da kayan ainci, ta tara $21bn a watanni 34 - Emefiele
Source: Depositphotos

Yayinda yake magana kan ci gaban ma’aikatar kudi, ya bayyana cewa zasu ci gaba da rage yawan dogaro da shigo da kayayyakin waje.

KU KARANTA KUMA: Dansadau ya fara kamfen, ya sha alwashin kawo karshen fashin shanu a Zamfara

A fannin noma, ya bayyana cewa shirin bayar da aro, ya bayar da tabbacin cewa Najeriya ta fita daga dogaro da shinkafar waje inda a yanzu take samar da shinkafa sosai harma ta ke sayarwa da kasashen ketare.

A watan Oktoba 2018, ya ce, manoma 862,069 da suka noma abinci daban-daban kusan nauyi 16 a fadin kasar, sun amfana daga shirin aron, wanda ya samar da ayyuka 2,502,675 a fadin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel