Na yi alkawarin samar da wutar lantarki awa 24 – Inji yar takarar shugaban kasa

Na yi alkawarin samar da wutar lantarki awa 24 – Inji yar takarar shugaban kasa

Tsohuwar minista, kuma yar takarar shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2019, Uwargida Oby Ezekwesil ta dauki alkawarin samar da wutar lantarki na dindindin a Najeriya idan har ta samu nasara a zaben shekarar 2019.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Uwargida Oby ta fito takarar shugaban kasa ne a karkashin inuwar jam’iyyar ‘Allied Congress Party of Nigeria – ACPN, inda ta bayyana cewa burinta shine ta samar da dawwamammen wutar lantarki ga garuruwa da biranen Najeriya.

KU KARANTA: Wa’iyazubillahi: Kotu ta yanke hukuncin kisa ga jigon APC saboda laifin wulakanta Al-Qur’ani

Na yi alkawarin samar da wutar lantarki awa 24 – Inji yar takarar shugaban kasa

Oby E.
Source: Depositphotos

“Daga shekarar 1999 zuwa yanzu, duk wani hasashen da gwamnatin tayi na kara adadin lantarki zuwa 6000MW, zuwa 20,000MW an kasa cikashi, gashi kuma yan Najeriya nada bukatar wuta, kuma a shirye suke su biya kudin wuta, ana iya gane haka ne ta yadda suke sayan na’urorin janareta iri iri daban daban.

“Ku duba nawa suke biya wajen gyaran na’urorin nan, wannan matsalar rashin wutar ne yasa dole kamfanoni suke kashe makudan kudade, musamman ribar da suke samu a wajen sayan janareta da duk wata hanyar da zata sama musu da wuta.” Inji ta.

Bugu da kari Oby tace wannan muhimmin aiki da ta sa a gaba na samar da wutar lantarki shine zai samar da ayyuka ga dimbin matasan Najeriya masu kwazo, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

“Manufarmu shine mu fara samar da wuta a shiyyoyin Najeriya da suka hada da Lagos, Kano, Enugu, Birnin Kebbi, Aba,Minna,Gombe, Lokoja, Gusau, Jos, Yola, Abuja, Ilorin, Bini, Owerri, da kuma Ijebu-Ode, cikin shekara hudu na farko.

“Sauran biranen da zasu amfana da wannan aikin sune Calabar, Katsina, Warri, Ibadan, Ado-Ekiti, Maiduguri, Yenegoa, Damaturu, Osogbo, Bauchi, Dutse, Fatakwal, Kaduna, Sokoto, Akure, Makurdi, Abakaliki, Uyo, Jalingo da Ontsha, hakanan zamu fadada ayyukan zuwa kauyukan dake makwabtaka dasu.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel