Allah na da wani sako ga Najeriya - Osinbajo

Allah na da wani sako ga Najeriya - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Lahadi, 2 ga watan Nuwamba ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da godema Allah, sannan ya bukaci da su yi duba ga nan gaba cike da buri domin Allah yayi masu tanadi.

Osinbajo ya yi wannan jawabin ne a taron addu’an kashen shekara a Presidential Villa Chapel da ke Abuja, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Allah na da wani sako ga Najeriya - Osinbajo

Allah na da wani sako ga Najeriya - Osinbajo
Source: Facebook

Osinbajo wanda ya yi ikirarin cewa Allah na da sako ga yan Najeriya a watanni da shekaru masu zuwa ya bukacin al’umman kasar da su kasance masu hakuri da dauriya.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikatan majalisar dokoki na barazanar fara zanga-zanga

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, uwargidarsa Victoria, mataimakin gwamnan jihar Nassarawa, Silas Agara, Ministan Niger Delta, Usani Uguru Usani da sauran jami’an gwamnati.

A wani lamari na daban, mun ji cewa babban hadimin ministan cikin gida, Hon Aliyu Ibrahim Gebi, ya ce zaben shugaban kasa na 2019 shine fita na karhe da dan takarar shugaban kasa a PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar zai yi.

Gebi, wanda ya amsa tambayoyi daga yan jarida a jiya, Lahadi 2 ga watan Disamba a Abuja yace zaben ba zai zamo mafi wahala ba a tarihin kasar domin a cewarsa Buhari ne kadai dodon magauta a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel