Neman maslaha: Yadda Saraki ya shawo kan Gwamnan Kwara ya hakura da takarar kujerar Sanata

Neman maslaha: Yadda Saraki ya shawo kan Gwamnan Kwara ya hakura da takarar kujerar Sanata

Mun samu labarin abin da ya sa Gwamnan Jihar Kwara, Dr Abdulfattah Ahmed ya fasa neman kujerar Sanata a karkashin Jam’iyyar PDP. Yanzu dai PDP ta maidawa Sanata Rafiu Ibrahim tikiti domin ya koma kujerar sa a 2019.

Yadda Saraki ya shawo kan Gwamnan Kwara ya hakura da takarar kujerar Sanata

Saraki ya nemi Fatahi ya hakura da takarar Sanata saboda PDP ta lashe zabe
Source: UGC

Rafiu Ibrahim wanda yake wakiltar Kwara ta Kudu ya nemi takarar Gwamnan Jihar Kwara a PDP amma ya sha kashi a hannun wanda Bukola Saraki ya tsaida. Bayan haka kuma sai Gwamna Fatahi Ahmed ya fara harin kujera Sanatan.

Wannan biyu-babu ne ya nemi ya batawa Sanata Rafiu Ibrahim da Mutanen Mazabar sa rai ganin yadda Sanatan ya bar APC ya bi Bukola Saraki zuwa PDP. Yanzu dai Saraki ya shawo kan Gwamnan Jihar ya hakura da neman Sanata.

Duba da kuma yanayin da zaben da aka gudanar kwanaki a Mazabar Irepodun/Isin/Oke Ero/Ekiti ya kasance ta sa dole Bukola Saraki ya fara shirin sabon lissafi domin gudun PDP ta sha kasa a Yankin a babban zaben da za a yi a 2019.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta rasa wani babban kusa a Kudancin Najeriya daf da zaben 2019

Daily Trust ta rahoto cewa Bukola Saraki bai ji dadin yadda PDP ta sha kashi hannun APC a zaben da aka yi kwanaki ba. Wannan ya sa Saraki ya nemi Sanata Rafiu Ibrahim ya koma kan kujerar sa saboda a hadu ayi wa PDP aiki a zaben badi.

Babu mamaki Shugaban Majalisar kasar yayi wa Gwamna Fatahi, wanda tsohon Kwamishinan sa ne alkawarin wani mukami mai tsoka a sama idan PDP tayi nasara. Wannan ne dai sai sa ace babu wanda yayi wa PDP bore a Jihar.

Gwamna Ahmed ya rike Kwamishinan kudi na shekaru 8 kafin ya zama Gwamna. Wannan ya sa Mutanen Garin su Sanata Rafiu Ibrahim su ke ganin ya kamata a ba su dama su sake aika wakilin su na akalla shekaru 4 a Majalisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel