Yajin aiki: Mun shiryawa Gwamnatin Tarayya tsaf – Inji Kungiyar ASUU

Yajin aiki: Mun shiryawa Gwamnatin Tarayya tsaf – Inji Kungiyar ASUU

- Gwamnatin Tarayya tayi barazanar dakatar da albashin Malaman Jami’o’i

- Yanzu dai Gwamnatin Kasar ta janye wannan mataki da tayi niyyar dauka

- Kungiyar ASUU tace a shirya ta ke da a dakatar da biyan ‘Ya ‘yan ta albashi

Yajin aiki: Mun shiryawa Gwamnatin Tarayya tsaf – Inji Kungiyar ASUU

Shugaban Kungiyar ASUU yace za su cigaba da yaji har sai Gwamnati tayi abin da ya dace
Source: UGC

Har yanzu dai Malaman Jami’a su na cigaba da gudanar da yajin aiki a fadin Najeriya. Wannan ya sa kwanaki Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar NUC da ke kula da Jami’o’i ta nemi a dakatar da albashin Malaman Makarantar.

Yanzu dai Gwamnatin Kasar ta janye wannan barazana na daina biyan Malaman Jami’o’in albashi. Shugaban Kungiyar ASUU na kasa watau Farfesa Biodun Ogunyemi bayyana wannan a wani dogon jawabi da ya fitar kwanan nan.

KU KARANTA: Gaskiyar magana; Abin da ya hana Atiku zuwa Kasar Amurka

Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa a shirya ASUU ta ke ta cigaba da yaji ko da kuwa Gwamnatin Najeriya za ta hana su albashin su. Ogunyemi ya nemi ‘Ya ‘yan ASUU su jajirce har sai sun kai ga nasara a gwagwarmayar da su ke yi.

Farfesa Ogunyemi ya dai jinjinawa ‘Yan kungiyar na ASUU tare da kara jan hankalin Malaman Jami’a da su guji shiga aji ko ofis ko gudanar da duk wani aiki na koyar da Dalibai a cikin Makarantun Jami’a har sai an shawo kan lamarin.

ASUU ta tabbatar da cewa za ta hukunta duk wanda ta samu yana sabawa wannan ka’idoji ko da a Jami’o’in da ba na Gwamnati bane. Yanzu dai ana sa rai yau Litinin ne za a cigaba da zama da Gwamnati domin duba bukatun na su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel