Atiku zai dauki kashin sa a hannu a zaben 2019 - Inji wani tsohon 'Dan Majalisa

Atiku zai dauki kashin sa a hannu a zaben 2019 - Inji wani tsohon 'Dan Majalisa

Babban hadimin ministan cikin gida, Hon Aliyu Ibrahim Gebi, ya ce zaben shugaban kasa na 2019 shine fita na karhe da dan takarar shugaban kasa a PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar zai yi.

Gebi, wanda ya amsa tambayoyi daga yan jarida a jiya, Lahadi 2 ga watan Disamba a Abuja yace zaben ba zai zamo mafi wahala ba a tarihin kasar domin a cewarsa Buhari ne kadai dodon magauta a zaben 2019.

Atiku zai dauki kashin sa a hannu a zaben 2019 - Inji wani tsohon 'Dan Majalisa

Atiku zai dauki kashin sa a hannu a zaben 2019 - Inji wani tsohon 'Dan Majalisa
Source: Depositphotos

Yana martani ne akan tambayar ko Wazirin Adamawa zai zamo barazana ga kudirin shugaba Buhari.

KU KARANTA KUMA: Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da ya sa Atiku bai tafi Amurka ba

Jigon na APC daga jihar Bauchi kuma shugaban kwamitin majalisar wakilai kan tsaro yace Atiku zai kwashi kashinsa a hannu a zaben 2019, inda yace zaben shugaban kasa zai zoma Buhari da APC kamar lomar abinci.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Wani shahararren dan kasuwa a Kebbi, Alhaji Mustapha Asaija, da wasu mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dubu biyar sun bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Sanata Isa Galaudu, dan takarar kujeran gwamna a PDP, da mataimakinsa, Alhaji Abubakar Malan, jami’ansu da yan jam’iyyar adawa da dama a jihar ne suka tarbi dan kasuwar da magoya bayansa a Ambursa da ke karaar hukumar Birnin Kebbi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel