Dumo Lulu-Briggs ya tsere daga Jam’iyyar APC a Jihar Ribas

Dumo Lulu-Briggs ya tsere daga Jam’iyyar APC a Jihar Ribas

Mun samu labari daga Jaridar This Day ta kasar nan cewa wani babban Jigon APC a Ribas ya fice daga Jam’iyyar. Wannan ba kowa bane dai illa tsohon ‘Dan takarar Gwamnan Jihar Dumo Lulu-Briggs.

Dumo Lulu-Briggs ya tsere daga Jam’iyyar APC a Jihar Ribas

Akwai zalunci da rashin adalci da kuma baba-kere a APC - Lulu Briggs
Source: UGC

Cif Dumo Lulu-Briggs wanda babban ‘Dan siyasa ne da ake ji da shi a Jihar Ribas ya bar Jam’iyyar APC ne bayan rikicin cikin-gida ya kunno kai a cikin Jihar. Lulu-Briggs yace babu yadda ya iya, amma dolen sa ya tattara kayan sa ya bar APC.

‘Dan siyasar ya shiga APC ne a bara inda ya hada-kai da tsohon Gwamnann Jihar Chibuike Rotimi Amaechi wanda a yanzu yake rike da mukamin Minista a Gwamnatin Buhari. Sai dai Lulu Briggs yace akwai wala-wala a tafiyar Jam’iyyar.

KU KARANTA: Rikici na nema ya kaure tsakanin Oshiomhole da Amaechi

Tsohon ‘Dan takarar Gwamnan Ribas din ya bayyana cewa sun yi kokarin kubutar da Jam’iyyar APC adawar a Jihar daga zalunci da kuma baba-kere amma hakan bai yiwu ba, inda yace a dalilin wannan ya fice daga Jam’iyyar ta APC.

Babban Alkalin kuma Hamshakin ‘Dan kasuwan mai, ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP a Jihar tana hannun mutum guda ne inda yake nufin Gwamna Nyesom Wike. Hakan dai ta sa Lulu Briggs yayi watsi da shawarar komawa PDP.

Sai dai mun ji kishin-kishin din cewa Cif Lulu Briggs ya samu tikiti a Jam’iyyar Accord Party inda zai sake yin takarar Gwamna a zaben 2019. Briggs zai kara ne da Tony Cole na APC da kuma Gwamna Nyesom Wike da ke kan mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel