Ma’aikatan majalisar dokoki na barazanar fara zanga-zanga

Ma’aikatan majalisar dokoki na barazanar fara zanga-zanga

Ma’aikatan majalisar dokokin kasar a karkashin inuwar kungiyar PASAN ta sanya 4 ga watan Disamba a matsayin ranar da za su gudanar da zanga-zanga a farfajiyar majalisar don bayyana fushinsu kan rashin biyansu albashi.

A cewar wata sanarwa daga sakataren kungiyar, Suleiman Haruna a Abuja, ya bayyana cewa mambobin kungiyar ta PASAN za su ci gaba da zanga-zanga na tsawon yini 5 (4 zuwa 8 ga watan Disamba) sakamakon abinda suka kira da yin shakulatan bangaro da shugabancin majalisar dokokin kasar ke yi da hakkokinsu.

Ma’aikatan majalisar dokoki na barazanar fara zanga-zanga

Ma’aikatan majalisar dokoki na barazanar fara zanga-zanga
Source: Depositphotos

A cewar Sakataren, mambobin kungiyar PASAN za su aiwatar da wannan zanga-zanga ne a wadannan rana da suka ambata daga karfe 8:00 na safe zuwa 2:00 na rana.

KU KARANTA KUMA: Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da ya sa Atiku bai tafi Amurka ba

Cikin wasu matsalolin da sakataren ya ambata suna ci wa ma’aiakatan majalisar wakilan Najeriyan sun hada da; Kin aiwatar da tsarin albashin ma’aiakatan majalisa.

Sannan kuma ana kin yi wa ma’aikata karin girma, inda suka so da a tabbatar da aikewa duk wanda ya cancaci karin matsayi takardarsa tare da biyansa karin albashinsa kafin nan kafin 31 ga Disamba.

Kungiyar dai ta baiwa majalisa makonni biyu ta aitar da wannan bukata ta so ko kuma ta

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel