Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da ya sa Atiku bai tafi Amurka ba

Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da ya sa Atiku bai tafi Amurka ba

An samu rade-radi, muhawara da suka daban-daban a kafofin watsa labarai tun bayan dad an takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya samu bizar shiga kasar Amurka a makon da ya gabata.

Rahotanni sun kawo cewa Atiku wanda ke da muradin ganin ya zama shugaban kasa a 2019, a ranar Alhamis ya bar kasar zuwa Ingila, bayan ya mallaki bizar sa sannan kum cewa ya shirya zuwa Amurka domin kore shakkun abokan adawarsa da suka yi zargin cewa ba zai iya shiga Amurka ba tare da an kama shi ba saboda rashawa.

A ranar Lahadi, jaridar Thecable ta tattaro daga majiyoyi dalilan da suka sanya Atiku bai tafi Amurka ba kamar yadda aka shirya.

Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da ya sa Atiku bai tafi Amurka ba

Ta bayyana: Gaskiyar dalilin da ya sa Atiku bai tafi Amurka ba
Source: Twitter

Majiyoyin nasu sun bayyana cewa dawowar Atiku ya kasance saboda kaddamar da kamfen dinsa na shugaban kasa, wanda shi (Atiku) ne uban tafiya, kuma ba zai iya kin halartan wannan taro ba a ranar Litinin.

KU KARANTA KUMA: Kasar Ingila Atiku ya tafi ba Amurka ba inji babban Hadimin sa

“Babu shakka zai tafi Amurka amma ba zai yiwu a fara kamfen a bayan idanunsa ba. Hakan zai kasance abun dariya”, wata majiya.

Wata majiya ma ta bayyana cewa Atiku ya fasa zuwa Amurka ne saboda bai samu tabbacin cewa ba za’a tozarta shi akan zargin rashawa da ake yi masa ba wanda akan shi ne aka tsare William Jefferson da Siemens. A koda yaushe yana karyata zargin.

Sai dai daya daga cikin hadimana ya fada ma The Cable cewa Atiku bai samu zuwa Amurka bane saboda ba za’a fara kamfen din shugaban kasa na PDP a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba a Sokoto.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel