2019: Atiku ya yi muhimman nade-nade guda 4

2019: Atiku ya yi muhimman nade-nade guda 4

A yayin da jam'iyyar PDP ta kammala shirin kaddamar da yakin neman zabenta gobe, Litinin, a jihar Sokoto, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar, Atiku Abubakar, ya nada maza uku da mace daya a matsayin mataimakansa na musamman.

Sanarwar nade-naden guda 4 na cikin wata sanarwa da Paul Ibe, mai taimakawa Atiku a bangaren yada labarai ya fitar a yau, Lahadi.

Mutanen da Atiku ya nada su ne; Ahmed Adamu, wanda zai kasance mai taimakawa Atiku a bangaren harkar matasa da tsare-tsare; Aliyu Bin Abbas, mataimaki na musamman ga Atiku a bangaren harkar matasa da kungiyoyi; Phrank Shuaibu, mai taimakawa na musamman a bangaren hulda da jama'a; da Funmi Lamuye, mai taimakawa ta musamman ga Atiku a yankin kudu maso yamma.

Mista Adamu, mai shekaru 33, dan asalin jihar Katsina, shine wanda ya kafa wata kungiyar kasa da kasa "Global President of Commonwealth Youth Council.

2019: Atiku ya yi muhimman nade-nade guda 4

Atiku
Source: Depositphotos

Mista Abba, mai shekaru 34, dan asalin jihar Borno, ya kasance darektan kungiyar ACF (Atiku Cares Foundation) da Atiku ya kafa domin taimakon ma su karamin karfi a yankin arewa maso gabas.

DUBA WANNAN: Yunkurin Atiku na shiga Amurka ya gamu da cikas, ya dawo Najeriya

Mista Shuaibu, mai shekaru 43, dan asalin jihar Kogi, ya kasance mai bayar da shawara ga 'yan siyasa da dama a baya. Ya taba rike mukamin mai taimakawa gwamnan jihar Kogi a bangaren hulda da jama'a, kasancewar sa kwararre a iya magana da sarrafa kalamai.

Uwargida Lamuye, lauya ce, 'yar asalin jihar Osun da kafin nadinta ta ke zaman mamba a hukumar majalisar tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel