Badakala: EFCC ta kara gano kadarorin biliyoyi na tsohon gwamnan PDP daga arewa

Badakala: EFCC ta kara gano kadarorin biliyoyi na tsohon gwamnan PDP daga arewa

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin (EFCC) ta sanar da cewar ta kara gano wasu kadarori biyu da darajar kowanne ta wuce miliyan N500 mallakar tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang.

A wata sanarwa da EFCC ta fitar a yay, Lahadi, ta ce ta gano gidaje guda biyu a fuloti mai lamba 8 da 9 a unguwar Rimi GRA da ke cikin garin Kaduna.

Tony Orilade, mukaddashin kakakin hukumar EFCC ta ce binciken binciken da su ka gudanar ya nuna ma su cewar an sayi kadarorin ta hanyar amfani da wani kamfani suna Nigerian Development Company (NNDC) da ke Kaduna.

Badakala: EFCC ta kara gano kadarorin biliyoyi na tsohon gwamnan PDP daga arewa

Jonah Jang
Source: Depositphotos

Ya kara da cewar tun a ranar 7 ga watan Mayu, 2018, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan bisa zarginsa da badakalar kudin da yawansu ya kai N6.3bn.

Jang, sanata mai wakiltar jihar Filato ta tsakiya a majalisar dattijai ta kasa, na fuskantar tuhumar almundahana da almubazzaranci da dukiyar jama'ar Filato da jihar ta karba daga babban bankin kasa (CBN) lokacin yana gwamna.

DUBA WANNAN: Tsakanin Atiku da gwamnonin PDP: Har yanzu da sauran rina a kaba

EFCC ta ce tsohon gwamnan ya tafka almundahana da kudin jihar Filato da yawansu ya kai N4.3bn ta hanyar amfani da sakataren gwamnatinsa, Yusuf Pam.

Daya daga cikin tuhumar da ake yiwa gwamnan ta nuna yadda ya karkatar da N2bn kudin tallafin ma su matsakaita da kananun masana'antu da CBN ta bawa jihar sa kafin karewar wa'adinsa a watan Afrilu na shekarar 2015.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel