'Yan ta'adda 2 sun kashe kan-su da bam a Garin Maiduguri – Sojojin Najeriya

'Yan ta'adda 2 sun kashe kan-su da bam a Garin Maiduguri – Sojojin Najeriya

Mun samu labari dazu nan daga bakin Rundunar Sojojin Najeriya cewa wasu mutane 2 ‘Yan kunar bakin wake sun sheka lahira bayan sun yi kokarin tada bam a Garin Maiduguri da ke cikin Jihar Borno.

Wasu mutane 2 sun kashe kan-su da bam a Garin Maiduguri – Sojojin Najeriya

Masu kunar bakin wake sun nemi su aukawa Sojojin Najeriya
Source: UGC

Wani namiji da kuma ‘yar uwar sa mace sun auka barzahu a Jihar Borno ta Yankin Arewa maso Gabas bayan yunkurin sakin bam a cikin wata Rundunar Sojojin Najeriya. Wannan mummuan abu ya faru ne a jiya da daddare,

‘Yan ta’addan wanda yanzu sun mutu, sun yi kokarin tada bam-baman da ke jikin su ne amma ba su yi nasara ba. Sai dai an yi rashin sa’a, wasu ‘Yan kato-da-goro har mutum 5 sun raunata daga wannan harin da aka kai.

KU KARANTA: Mutane 2 sun mutu bayan bada shaida kan wani tsohon Gwamna

‘Yan ta’addan sun nemi su yi mutuwar kasko ne tare da Rundunar Bataliya ta 195 ta Dakarun Sojojin Najeriya. Allah dai ya tsaga da sauran kwanan Sojojin bayan da bam din ya tashi da ‘Yan ta’addan ba tare da ya kashe kowa ba.

Jami’an tsaro da masu bada agaji sun mamaye wurin da wannan abu ya faru a cikin Garin Maiduguri inda aka kuma ruga da wadanda harin ya shafa zuwa babban asibitin da ke cikin Hedikwatar Sojojin Najeriya da ke Jihar Borno.

Rundunar Sojojin kasar ne su ka bada wannan sanarwa a shafin su na Tuwita. Wannan abu ya faru ne da kimanin karfe 8:00 na daren jiya Asabar 1 ga Watan Disamban nan a kusa da wani Gareji da ke cikin Garin Maiduguri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel