Tsakanin Atiku da gwamnonin PDP: Har yanzu da sauran rina a kaba

Tsakanin Atiku da gwamnonin PDP: Har yanzu da sauran rina a kaba

Rashin ganin fuskokin gwamnonin PDP, musamman na yankin kudu maso gabas, a wurin bikin nadin Atiku a matsayin wazirin Adamawa ya kara tabbatar da cewar har yanzu akwai babbar baraka a tsakaninsu.

Alamu na nuna cewar har gwamnonin yankin na cikin kokonton dan takarar da zasu goyawa baya tsakanin Atiku a PDP da shugaba Buhari a APC.

Ma su bibiyar al'amuran siyasar PDP a kasa sun gano cewar tun bayan da kotu ta tabbatar da Ahmed Makarfi a matsayin halastaccen shugaban PDP, gwamnonin yankin kudu maso gabas ke baya-baya da harkokin jam'iyyar.

Hakan ta kara bayyana a fili bayan fuskantar cewar gwamnonin na kauracewa duk wani taro na jam'iyyar PDP tare da yawan ganinsu na kai ziyara fadar shugaban kasa, lamarin da ya kara rurar wutar zargin cewar gwamnonin na goyon bayan takarar shugaba Buhari.

Tsakanin Atiku da gwamnonin PDP: Har yanzu da sauran rina a kaba

Gwamnonin yankin kudu maso gabas
Source: UGC

Da farko an yi tunanin cewar gwamnonin za su goyawa Atiku baya bayan ya zabi Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, a matsayin dan takarar mataimakinsa, amma sai ga shi har yanzu basu nuna alamun suna tare da Atiku ba a zahiri.

Rahotanni sun bayyana cewar gwamnonin tare da hadin kan mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, sun hade kansu tare da juyawa takarar Atiku baya a kan zabin Obi a matsayin dan takararsa na mataimaki.

DUBA WANNAN: Yunkurin Atiku na shiga Amurka ya gamu da cikas, ya dawo Najeriya

Gwamnonin da jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar PDP daga cikin 'yan kabilar Igbo sun fusata ne saboda Atiku bai tuntube su ba kafin ya zabi Obi a matsayin abokin takarar sa.

Duk kokarin Obi na ganin ya shawo kan gwamnonin ta hanyar ziyartar su har gidajensu bai canja halayyar su ga takarar Atiku ba.

Daga cikin jihohi 5 da yankin kudu maso na 'yan kabilar Igbo ke da su, PDP na mulki a jihohi uku da su ka hada da; Enugu, Abiya, da Ebonyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel