Kasar Ingila Atiku ya tafi ba Amurka ba inji babban Hadimin sa

Kasar Ingila Atiku ya tafi ba Amurka ba inji babban Hadimin sa

Mun samu labari ba da dadewa ba, akasin rade-radin da yake yawo na cewa ‘Dan takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sheka zuwa Kasar Amurka bayan ya samu takardun biza.

Kasar Ingila Atiku ya tafi ba Amurka ba inji babban Hadimin sa

'Dan takarar Shugaban kasa Atiku ya karyata batun zuwan sa Amurka
Source: Depositphotos

Atiku ya karyata rahoton Jaridar The Cable na cewa ya tafi Kasar Amurka, jim kadan da Kasar ta ba shi takardun shiga bayan yayi shekara da shekaru da haramta masa zuwa Kasar saboda zargin sa da ake yi da aikata wasu laifuffuka.

Atiku Abubakar yayi wannan jawabi ne ta bakin wani Hadimin sa, Paul Ibe. Ibe ya fadawa Jaridar Leadership cewa Atiku ya tafi Kasar Ingila ne domin wata ziyara mai zaman kan-ta. Ibe yace sam ba Amurka Mai gidan sa ya tafi ba.

KU KARANTA: Ana rade-radin jirgin Atiku ya dawo gida bayan ya gaza shiga Amurka

Mista Paul Ibe yace a Ranar Litinin dinnan 3 ga Watan Disamban 2018, Atiku zai dawo gida Najeriya domin fara yakin neman zabe gadan-gadan. Ibe yace Atiku zai soma fara kamfen din sa ne daga Jihar Sokoto a gobe da safe.

Hadimin ‘Dan takarar Shugaban kasar na Jam’iyyar PDP ya bayyana cewa Atiku ya tafi Ingila ne domin yayi wasu harkokin gaban sa. Gwamnatin Najeriya dai ta tabbatar da cewa Atiku na kokarin neman takardun shiga Amurka.

Kwanakin baya Dr. Doyin Okupe ya tabbatar da cewa a karshen Watan jiya Atiku Abubakar zai shiga Kasar Amurka. Har yanzu dai da alamu tsohon Mataimakin Shugaban kasar na Najeriya bai shawo ta da Kasar ta Amurka ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel