Bukukuwan Kirismeti: CBN na neman takawa tashin Dalar Amurka burki

Bukukuwan Kirismeti: CBN na neman takawa tashin Dalar Amurka burki

Labarin da mu ke ji a yanzu shi ne, Babban bankin Najeriya watau CBN na kokarin ceto Naira bayan darajar kudin na Najeriya yayi kasa matuka kwanan nan. Yanzu dai Dalar Amurka ta doshi N370 a Najeriya.

Bukukuwan Kirismeti: CBN na neman takawa tashin Dalar Amurka burki

Darajar Naira ta gangara kasa ainun a cikin ‘yan kwanaki kadan
Source: Depositphotos

A Ranar Juma’ar nan da ta wuce, an saida Dalar Amurka a kan kudi N371. Ana kuma tunani Dalar na iya haura wannan farashi kafin karshen wannan shekarar. Bukukuwan kirismeti dai za su iya sa darajar Dalar ta sake tashi.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa ‘Yan kasuwar canji sun fara saida Dala 1 a kan sama da N370 a cikin wannan Watan na Disamba. Hakan ta sa babban bankin Kasar na CBN ke kokarin ganin an rage tashin da Dalar ke yi.

KU KARANTA: Lamarin Atiku na neman izinin shiga kasar Amurka abu ne sirri - Jakadan Amurka

CBN za ta rika sakin Daloli a kasuwa har sau 4 a mako domin ganin an sanyawa Dalar Amurkar takunkumi. A Ranar Talatar nan ne ma CBN ta dumbuzo Dala Miliyan 210 a hannun ‘yan kasuwa domin takaita saukar Naira.

CBN kan saki makudan Daloli a Ranar Litinin da Laraba da kuma Juma’a domin hana Dalar yi wa Naira fintikau. Yanzu kuma ma dai CBN din za ta rika watso Dala 15, 000 a duk Ranar Alhamis domin a rage hauhawar farashin ta.

Yanzu dai ana saida Dalar found ta Ingila ne a kan N472, yayin da kuma Euro ta kai N415. Asusun kudin kasar wajen Najeriya kuma ya haura Dala Biliyan 42 duk da canjin farashin mai kamar yadda babban bankin kasar ya bayyana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel