Yunkurin Atiku na shiga Amurka ya gamu da cikas, ya dawo Najeriya

Yunkurin Atiku na shiga Amurka ya gamu da cikas, ya dawo Najeriya

Wata kungiya mai suna "Initiative To Save Democracy" ta ce tana da sahihan bayanai cewar dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya dawo Najeriya bayan gaza samun tabbaci daga bangaren shari'a na Amurka kan cewar ba za a kama shi ba idan ya shiga kasar.

Jaridar The Cable ta rawaito cewar Atiku ya samu bizar shiga Amurka tare da bayyana cewar ya tashi zuwa kasar Ingila, inda daga bisani zai wuce kasar ta Amurka a karo na farko bayan shekaru 13.

Kungiyar ta bayyana cewar Atiku ya tashi zuwa kasar Ingila ne da niyyar wucewa zuwa Amurka bayan kasar ta bashi biza.

"Manufar sa ta zuwa Ingila shine domin kasar ta taimaka ma sa wajen samun tabbacin cewar sashen shari'a na Amurka ba zai kama shi ba idan ya shiga kasar. Sai gwamnatin kasar ta Ingila ta shaida ma sa cewar ba za ta iya bashi tabbacin cewar sashen shari'ar ba zai kama shi ba idan ya shiga kasar," a cewar kungiyar.

Yunkurin Atiku na shiga Amurka ya gamu da cikas, ya dawo Najeriya

Atiku
Source: Twitter

Gwamnatin kasar Amurka ta saka Atiku cikin jerin sunayen mutanen da zata tuhuma duk lokacin da ya shiga kasar a kan zargin badakalar kudi da jawo hukunta, William Jefferson, dan majalisar kasar Amurka.

DUBA WANNAN: Dan takarar shugaban kasa ya koma APC, ya goyawa Buhari baya

Gaza samun tabbacin cewar ba za a kama shi ba idan ya shiga Amurka, Atiku ya gaggauta dawowa Najeriya domin gudun kar ya shiga kasar a samu matsala.

Paul Ibe, mukaddashin shugaban sashen yada labarai na ofishin kamfen din Atiku, ya tabbatar da cewar tuni Atiku dawo Najeriya, a wani sako da ya fitar a shafinsa na Tuwita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel