Zan bayar da tallafi ga Manoman da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a bana - Buhari

Zan bayar da tallafi ga Manoman da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a bana - Buhari

Mun samu cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin aiwatar da waiwaye na arziki inda gwamnatinsa za ta bayar da tallafi ga manoma domin rangwanta ma su dangane da asarar da ambaliyar ruwa ta yi ma su sanadi a daminar bana.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin wani sako yayin taron ranar manoma na wannan shekara ta 2018 da aka gudanar a yau Asabar cikin babban birnin Yenagoa na jihar Bayelsa, wanda kamfanin man fetur na AGIP ya dauki nauyi domin Manoman jihar Rivers, Bayelsa, Delta da kuma Imo.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaban kasar ya bayyana hakan ne da sanadin kakakin sa Mista Femi Adesina inda ya bayyana cewa, cibiyar kula da harkokin abinci ta Najeriya ta bayar da sahalewarta kan bayar da tallafi ga Manoma da Masunta da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a daminar bana.

Zan bayar da tallafi ga Manoman da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a bana - Buhari

Zan bayar da tallafi ga Manoman da ambaliyar ruwa ta yiwa barna a bana - Buhari
Source: Depositphotos

Shugaba Buhari ya kuma janyo hankalin Matasa wajen mayar da hankali da kuma bayar da himma akan tsagwaran kishin kasar su da ko shakka ba bu cimma nasarar ta za ta fa'idantu ga manyan gobe da masu tasowa.

KARANTA KUMA: Harkar Tsaro na kara tabarbarewa a jihar Bayelsa - Gwamna Dickson

A yayin da yake yabawa Manoman, shugaba Buhari ya kuma bayyana farin cikin sa dangane da yadda kasar nan ke kan gaba ta wadatuwa da kayan abinci musamman amfanin gona da zai inganta tattalin arzikin kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a Yammacin yau na Asabar shugaba Buhari ya shilla kasar Poland domin halartar taron majalisar dinkin duniyar reshen kula da harkokin sauyi yanayi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel