2019: Yan APC da dama na shirin barin jam’iyyar a Benue kan wanda zai yi mataimakin gwamna

2019: Yan APC da dama na shirin barin jam’iyyar a Benue kan wanda zai yi mataimakin gwamna

Akalla mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Benue 10,000 ne ke shirin barin jam’iyyar zuwa Peoples Democratic Party (PDP) gabannin zaben 2019.

A cewar wa majiya, shugabannin kananan hukumomi takwas na jam’iyyar daga yankuna uku na jihar sun kammala shiri tare da magoya bayansu don barin jam’iyyar saboda shugaban jam’iyyar ya zabi Sam Ode a matsayin dan takarar mataimakin gwamnan jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Shugabannin sun bayyana cewa shawarar da shugaban jam’iyyar ya dauka na watsar da Dr. Dickson Akoh don daukar tsohon ministan Niger Delta, Sam Ode a matsayin mataimakin gwamna a zaben 2019 babban cin fuska ne a gare su, inda suka ce Sam Ode ya kasance dan PDP da bai taba halarta kowani taro na APC ba a jihar har sai da aka zo wajen zabar mataimakin gwamna.

2019: Yan APC da daman a shirin barin jam’iyyar a Benue kan wanda zai yi mataimakin gwamna

2019: Yan APC da daman a shirin barin jam’iyyar a Benue kan wanda zai yi mataimakin gwamna
Source: Twitter

Shugabannin kananan hukumomin sun bayyana cewa APC a Benue bata dauki batun lashe jihar ba da muhimmanci a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tawagar mata na kungiyar kwallon kafan Najeriya su yi nasarar lashe wasan matan Afrika

Daya daga cikin shugabannin kananan hukumomin APC din ya ce gara ace yayiwa gwamna mai ci Samuel Ortom biyayya da ace yayi aiki da Sam de a matsayin mataimakin Jime a zabe mai zuwa.

Yace da alama shugaban jam’iyyar bai yi nadama kan abunda ya faru a baya ba musamman bayan sauya shekar gwamna mai ci, Samuel Ortom zuwa PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel