Buhari ya isa kasar Poland lafiya, hotuna

Buhari ya isa kasar Poland lafiya, hotuna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka lafiya a kasar Poland bayan ya bar Najeriya yau, Asabar, domin wani halarta wani taro a kan canjin yanayi.

Legit.ng ta kawo ma ku rahoton cewar shugaba Buhari ya tashi daga babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja zuwa kasar Poland domin halartan taron canjin yanayi.

Tun da farko, mun kawo ma ku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja domin zuwa birnin Katowice, kasar Poland, rana Asabar domin halartan taron gangamin duniya kan canjin yanayi karo na 24 na majalisar dinkin duniya wato UNFCCC.

Buhari ya isa kasar Poland lafiya, hotuna

Buhari ya isa kasar Poland lafiya
Source: Twitter

Buhari ya isa kasar Poland lafiya, hotuna

Buhari a kasar Poland
Source: Twitter

Buhari ya isa kasar Poland lafiya, hotuna

Buhari ya isa kasar Poland lafiya
Source: Twitter

Wannan taro na shugabannin duniya zai gudana ne daga rana 2 ga watan Disamba zuwa 5. Game da cewar wadanda suka shirya taro, ana kyautata zaton kammala magana kan aiwatar da shawarwarin da ke cikin yarjejeniyar canjin yanayi da akayi a kasar Faransa wato "Yarjejeniyar Paris".

Yayin taron, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai gabatar da jawabi kan irin namijin kokarin da gwamnatin Najeriya keyi wajen dakile canjin yanayi ta hanar aiwatar da ayyukan da ta shirya.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Borno ta bawa sojoji 5 kyautar manyan motoci, hotuna

Bayan hakan, Buhari zai gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland. Kana zai gana da shugaban kasar Poland, Andrzej Duda da firam ministan kasar Mateusz Morawiecki.

Daga cikin wadanda zasu takawa Buhari baya sune gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuwanyi; gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

Sauran sune ministan harkokin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama; ministan ayyukan ruwa, Suleiman Adamu, da karamin ministan yanayi, Ibrahim Jibrin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel