Dan takarar shugaban kasa ya koma APC, ya goyawa Buhari baya

Dan takarar shugaban kasa ya koma APC, ya goyawa Buhari baya

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar LP (Labour Party), Sam Nwanti, ya janye takarar sa tare da bayyana goyon bayansa ga tazarcen shugaba Buhari.

Mista Nwanti, dan asalin garin Mbieri, jihar Imo, da ke zaune a kasar Amurka, ya bayyana janyewa daga takarar ne yayin wani taro da manema labarai a garin Owerri, babban birnin jihar Imo.

Dan takarar shugaban kasa ya koma APC, ya goyawa Buhari baya

Dan takarar shugaban kasa ya koma APC, ya goyawa Buhari baya
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun yi karin haske a kan bayyanar wasu bakin 'yan bindiga a Sokoto

Da yake bayyana dalilin janyewar sa, Nwanti ya ce ya yanke shawarar fasa yin takarar ne domin karawa takarar shugaba Buhari baya sannan ya kara yin shirin fuskantar takarar da karfinsa a shekarar 2023.

"A yau, Asabar, na ke sanar da janye takarar neman shugaban kasar Najeriya a jam'iyyar LP tare da canja sheka zuwa jam'iyyar APC.

"Na dawo jam'iyyar APC ne domin goyon bayan tazarcen Buhari saboda yana bukatar goyon bayan jama'a irinmu domin ya samu ya karasa aiyukan alheri da ya fara. Zan taimaki jam'iyyar APC da gwamnatin shugaba Buhari, musamman a yakin da ya ke yi da cin hanci. Na janye don kar na kassara kuri'un da Buhari zai samu a 2019," a cewar Nwanti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel