A karshe: Atiku ya tashi zuwa kasar Amurka

A karshe: Atiku ya tashi zuwa kasar Amurka

Kasar Amurka ta bawa tsohon dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar izinin shiga kasar wato biza.

A cewar The Cable wani daga cikin iyalin tsohon shugaban kasan ya tabbatar da cewa an bashi takardan izinin shiga kasar.

A watan Oktoba, Direkta Janar na yakin neman zaben Atiku Presidential Campaign Organisation (APCO), Gbenga Daniel ya yi ikirarin cewa Amurka ta fadawa Atiku cewa zai iya neman bizar.

A karshe: Atiku ya tashi zuwa kasar Amurka

A karshe: Atiku ya tashi zuwa kasar Amurka
Source: Twitter

A yayin da ake yi tambaya a kan batun a ranar Juma'a, Jami'in hulda da jama'a na ofishin jakadancin Amurka da ke Legas, Brussel Brooks ba yi tsokaci kan batun ba inda ya ce sirri ne.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa zaben Atiku zai fi zama alheri ga 'yan Najeriya - Saraki

A baya, an ganin kamar Atiku ba zai iya shiga Amurka ba saboda ana zargin cewa ya hada baki da wani dan majalisa a Amurka, William Jefferson wajen karbar rashawa kuma shi dan majalisar an tabbatar da laifinsa a Amurka.

Duk da cewa Atiku ya jadada cewa bai aikata wani laifi ba, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta dade tana kallubalantarsa ya tafi Amurka idan har ya tabbatar bashi da laifin.

A ranar Alhamis, Ministan yada labarai na Najeriya, Lai Mohammed ya gargadi Amurka da kada da sake ta bawa Atiku visa idan har ba ta son nuna fifiko tsakanin 'yan takarar shugabancin kasa na shekarar 2019.

An ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin Amurka ta bawa Atiku izinin shiga kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel