Harin Metele: Hukumar soji za ta dauki matakin shari'a a kan wasu mutane

Harin Metele: Hukumar soji za ta dauki matakin shari'a a kan wasu mutane

Hukumar sojin Najeriya ta yi gargadi da kakkausar murya a kan ma su yada labaran karya da niyyar nuna gazawar dakarun a yakin da su ke yi da aiyukan ta'addanci a yankin arewa maso gabas.

A wata sanarwa da sabon darektan sashen hulda da jama'a na hukumar soji, Birgediya Sani Kukasheka Usman, rundunar sojin ta ce ma su yada adadin karya na sojojin Najeriya da aka kashe a harin Metele, na yin hakan ne domin yaudarar jama'a da niyyar kawo nakasu a zaben shekarar 2019.

Harin Metele: Hukumar soji za ta dauki matakin shari'a a kan wasu mutane

Harin Metele: Hukumar soji za ta dauki matakin shari'a a kan wasu mutane
Source: UGC

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa zaben Atiku zai fi zama alheri ga 'yan Najeriya - Saraki

Kukasheka ya kara da cewar har yanzu akwai wasu mutane da kafafen yada labarai da ke cigaba da yada alkaluman karya na sojin da aka kashe a harin Metele duk da karin haske da hukumar sojin ta yi a kan adadin dakarunta da aka kashe yayin harin.

"Tun a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2018, hukumar soji ta fitar tare da sanar da jama'a adadin dakarunta da su ka mutu sakamakon harin da aka kai sansanin soji da ke Metele.

"Za mu cigaba da sanar da jama'a a kan lokaci duk wani lamari da ya shafi hukumar soji," a cewar Kukasheka.

Kukasheka ya gargadi ma su yada labaran bogi da su nesanta kansu da hukumar soji tare da yin kira ga kafafen yada labarai da su zama ma su biyayya ga ka'idojin da dokokin aikinsu.

A cewar sa, hukumar soji ta gano wadanda ke yada labaran karya a kan harin na Metele tare da bayyana cewar rundunar soji za ta dauki matakin shari'a a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel