Harkar Tsaro na kara tabarbarewa a jihar Bayelsa - Gwamna Dickson

Harkar Tsaro na kara tabarbarewa a jihar Bayelsa - Gwamna Dickson

Mun samu cewa a karshen wannan mako da yayi daidai da farkon watan Dasumba na shekarar 2018, kusoshin gwamnatin jihar Bayelsa sun yi tir gami da Allah wadai dangane da tabarbarewa da tsanani na rashin tsaro a fadin jihar.

Kusoshin gwamnatin sun bayyana takaicinsu gami da damuwa dangane da yadda ake faman sauye-sauye na kwamishinan hukumar 'yan sanda na jihar kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito.

Cibiyar kusoshin gwamnatin ta kuma zargi 'yan adawa da haddasa wannan mummunan lamari a fadin jihar da a cewar ta sun dukufa wajen jagorantar hukumomin tsaro kan kaucewa turba ta adalci a madadin gwamnatin jihar.

Yayin kammala taron ta karo na 99 da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Yenagoa, cibiyar kusoshin gwamnatin ta bayyana cewa, 'yan adawa da hammaya ke da alhakin assasa tayar da zaune tsaye a jihar da kuma gurbata duk wani ingataccen tanadi yayin gabatowar babban zabe na 2019.

Gwamna jihar Bayelsa; Seriake Dickson

Gwamna jihar Bayelsa; Seriake Dickson
Source: Depositphotos

Taron da gwamnan jihar ya jagoranta, Seriake Dickson ya bayyana cewa, 'yan adawar gwamnatinsa na aikata babban laifi wajen siyasantar da tsaro da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali na al'ummar sa.

KARANTA KUMA: Hadin Kai tsakanin Musulmi da Kirista shine zaman lafiyar Najeriya - Buhari

Yayin ganawarsa da manema labarai bayan kammaluwar taron na majalisar kusoshin gwamnatin jihar, kwamishinan yada labarai na jihar, Daniel Iworiso Markson ya bayyana cewa, tabarbarewar rashin tsaro sakamakon dambarwar hargitsin siyasa ya sanya ake faman sauye-sauyen Kwamshinonin 'yan sanda a jihar.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsantsar rashin kunya ta sanya wasu 'yan fashi da makami sun bar sakon sunan nan dawowa bayan sun harzuka dangane da rashin samun masu gida yayin da suka fita cin kasuwarsu ta ta'addanci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel