IGP na tuhumar Saraki kan fashin Offa, shi kuma Malami yana kare shi, wanne ne ba wanne ba

IGP na tuhumar Saraki kan fashin Offa, shi kuma Malami yana kare shi, wanne ne ba wanne ba

- Anyi fashi a jihar Kwara da motocin gwamnati a tsakiyar shekarar nan

- An gano yaran Saraki ne 'yan dabar da suka aikata wannan

- Saraki yace sharri ne, wanda ya fadi sunansa ya mutu a hannun 'yansanda

IGP na tuhumar Saraki kan fashin Offa, shi kuma Malami yana kare shi, wanne ne ba wanne ba

IGP na tuhumar Saraki kan fashin Offa, shi kuma Malami yana kare shi, wanne ne ba wanne ba
Source: Depositphotos

Kuma ma dai, Antoni Janar na kasar nan, kuma babban lauyan gwamnati, ya sake rattabawa shugaban hukumar 'yansada wasika, cewa, kada ya kai Bukola Saraki kotu, domin kuwa babu wata hujja dake alakanta shi da fashin da aka yi a Kwara.

A baya dai anyi fashi ne kuma aka gano da motocin gwamnati ne aka yi fashin, kuma Saraki yana biyar yaran albashi a matsayinsu na 'yan bangar siyasa, sai dai babu hujja cewa shi ya sanya su suyi fashin.

An mayar da kes din Abuja, oishin IG, kuma lamarin yayi qamari, inda har ta kai Sarakin, da mukarrabansa da gwamnan Kwara, sun fice daga APC.

DUBA WANNAN: Yadda yara suka kashe Mamman Nur na Boko Haram

Shi kuma babban dan fashin, ya mutu a hannun 'yansanda, ana tsaka da bincikensa. Lamari da Sarakin yace akwai bi-ta da kulli.

Antoni Janar dai, shine mai hurumin shigar da qara da sunan gwamnatin Tarayya, shi kuma shugaban 'yansanda, shine shugaban bincike a kowanne laifi a kasar nan.

Saraki kuwa, shugaban majalisar dattawa ne, wanda kuwa shine na uku a kujerun mulki a kasar nan.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel