Okorocha ya bayar da umarnin kama manajojin bankunan jihar Imo a kan batun albashin ma'aikata

Okorocha ya bayar da umarnin kama manajojin bankunan jihar Imo a kan batun albashin ma'aikata

Gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha, ya bayar da umarnin dakatar da babban akawun jihar, Uwargida Stella Udogwu.

Kazalika, gwamnan ya bayar da umarnin kama manyan manajojin bankunan EcoBank da Access Bank saboda rashin biyan ma'aikata albashin watan Nuwamba.

Dakatar da babbar akawun jihar ta Imo ya fara aiki ne nan take, kamar yadda gwamna Rochas ya umarta.

Rochas ya bayyana cewar ya yi mamakin gano cewar ba a bi wannan umarni da ya dade da bayar wa ba.

Okorocha ya bayar da umarnin kama manajojin bankunan jihar Imo a kan batun albashin ma'aikata

Rochas Okorocha
Source: Getty Images

A sabuwar sanarwar, Rochas ya bayar da umarnin a biya ma'aikatan da matsalar ta shafa albashinsu na watan Nuwamba da Disamba a ranar 3 ga watan Disamba, kasancewar ranakun 1 da 2 ga Disamba ranakun hutu ne.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Borno ta bawa sojoji 5 kyautar manyan motoci, hotuna

Kazalika gwamnan ya amince da biyan dukkan ma'aikatan jihar Naira N10,000 a matsayin kyautar bikin Kirsimeti.

"Tun cikin sati na biyu a watan Oktoba na amince da biyan ma'aikata albashinsu. Dole a sakar wa ma'aikata albashinsu, har da na watan Disamba," a cewar Rochas, yayin gabatar da jawabi a wurin taron kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi (NULGE) na murnar cika shekaru 40 da kafuwa, wanda aka yi Hero's Square da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel