Rayuka 4 sun salwanta, Mutane 8 sun jikkata a wani Hatsari da ya auku a jihar Nasarawa

Rayuka 4 sun salwanta, Mutane 8 sun jikkata a wani Hatsari da ya auku a jihar Nasarawa

Za ku ji cewa a ranar Juma'ar da ta gabata, aukuwar wani mummunan hatsarin Mota a babbar hanyar garin Akwanga zuwa garin Nasarawa ya salwantar da rayukan Mutane 4 yayin da Mutane 8 suka jikkata kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Feustina Alagbe, shugaban hukumar FRSC mai kula da bayar da kariyar manyan hanyoyi reshen jihar, shine ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai na jaridar Daily Trust a ranar da ta gabace mu.

Rayuka 4 sun salwanta, Mutane 8 sun jikkata a wani Hatsari da ya auku a jihar Nasarawa

Rayuka 4 sun salwanta, Mutane 8 sun jikkata a wani Hatsari da ya auku a jihar Nasarawa
Source: Depositphotos

Mista Alagbe ya bayyana cewa, wannan mummunan hatsari ya auku a tsakanin wasu Motoci biyu kirar kamfanin Volkswagen Sharon da kuma samfurin Peugeot dauke da fasinjoji 12.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, an yi gaggawar garzaya da wadanda ibtila'in ya auku akan su zuwa asibitin kurkusa, inda Likitoci suka tabbatar da mutuwar 4 nan take.

KARANTA KUMA: 'Yan Takarar Gwamna 782 sun fara yakin neman zabe a yau Asabar

Ahmed Tukur, hadimi na musamman akan hulda da manema labarai ga gwamnan jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al Makura, na daya daga cikin wadanda karar kwana ba ta cimma su ba inda a halin su ke ci gaba da samun kulawa a babbar cibiyar lafiyar ta garin Keffi.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito ya bayyana cewa, aukuwar wani mummunan hatsari a ranar Alhamis din da ta gabata ya salwantar da rayukan Mutane 5 a babban birnin Abakaliki na jihar Enugu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel