'Yan Takarar Gwamna 782 sun fara yakin neman zabe a yau Asabar

'Yan Takarar Gwamna 782 sun fara yakin neman zabe a yau Asabar

Mun samu cewa 'Yan takarkaru na fiye da jam'iyyu 80 da za su fafata yayin babban zabe na 2019 sun kaddamar da yakinsu na neman zabe a yau Asabar kamar yadda rahotanni da sanadin shafin jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ko shakka ba bu akwai kimanin 'yan takara 782 manema kujerun gwamna da za su fafata cikin jihohi 28 dake fadin kasar nan kamar yadda binciken manema labarai ya tabbatar.

Rahotanni sun bayyana cewa, zabukan gwamna ba za su gudana ba cikin jihohi 7 da ke fadin kasar nan a yayin babban zaben na badi sakamakon sabanin kakar zabe da ya sanya tuni suka gudanar da na su a lokutan baya.

'Yan Takarar Gwamna 782 sun fara yakin neman zabe a yau Asabar

'Yan Takarar Gwamna 782 sun fara yakin neman zabe a yau Asabar
Source: Depositphotos

Jihohin bakwai da sai dai su ji ana yi yayin zaben badin sun hadar da Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Kogi, Ondo da kuma Osun.

Jadawalin tsare-tsaren hukumar zabe ta kasa ya kayyade cewa, za a fara gudanar da yakin neman zaben kujerun gwamnoni a ranar 1 ga watan Dasumba na shekarar 2018 da ta yi daidai da ranar yau ta Asabar.

KARANTA KUMA: Ba ni da laifi kan sace 'Yan Matan Chibok - Jonathan

Sashe na 99 cikin kundin tsaro na hukumar ya bayar da dama ta fara gudanar da yakin neman zabe kwanaki 90 kafin babban zabe, inda binciken manema labarai ya tabbatar da cewa mafi akasarin za su ribaci wannan lokaci na kaddamar da yakinsu.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin da Hausawa kan ce tun zafi-zafi ake dukan karfe, da yawan masu hankoron kujerun gwamna a fadin jihohin kasar nan za su kaddamar da yakokinsu a yau Asabar tare da zage dantse da daura damara ta cimma nasara a zaben kasa na badi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel