Wike ya fusata da Atiku, zai ajiye aikin yi ma sa kamfen

Wike ya fusata da Atiku, zai ajiye aikin yi ma sa kamfen

- Alamu ma su karfi na nuni da cewar gwamna Wike na jihar Ribas zai ajiye aikin yiwa Atiku kamfen

- Rahotanni sun bayyana cewar gwamna Wike ya fusata ne bayan an jingine shi gefe a tafiyar kamfen din Atiku

- Uche Secondus, shugaban jam'iyyar PDP, ne ya nada Wike da wasu ragowar 'yan jam'iyyar PDP a matsayin jagororin kamfen din Atiku

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, zai yi murabus daga matsayinsa na jagoran kamfen din Atiku a yankin kudu maso kudu.

Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewar Wike zai yi murabus ne saboda jin haushin yadda kwamitin kamfen din Atiku ya jingine shi gefe guda wajen gudanar da al'amuransa.

Abinda ya kara batawa gwamnan rai shine yadda aka nada wasu jama'a da zasu yi aiki tare da shi ba tare da ya an sanar da shi ba.

Wike ya fusata da Atiku, zai ajiye aikin yi ma sa kamfen

Wike da Atiku
Source: UGC

Uche Secondus, shugaban jam'iyyar PDP, ne ya nada Wike da wasu 'ya'yan jam'iyyar a matsayin jagororin kamfen din Atiku a sassan kasar nan, kwanaki kadan bayan lashe zaben fidda 'yan takara da Atiku ya yi.

DUBA WANNAN: Ramuwar gayya: Sojoji sun tashi wata maboyar 'yan Boko Haram

Bayan nada Wike a matsayin jagoran kamfen din Atiku a yankin kudu maso kudu, Secondus ya nada gwamnan jihar Gombe; Ibrahim Dankwambo, ya jagoranci kamfen din Atiku a yankin arewa maso gabas, gwamnan jihar Benuwe; Samuel Ortom, ya jagoranci yakin neman zaben Atiku a yankin arewa ta tsakiya, gwamnan jihar Ebonyi; Dave Umahi, jagora a yankin kudu maso gabas, da kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a matsayin jagoran kamfen din Atiku a yankin kudu maso yamma.

Gwamna Wike na daga cikin manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP da ke goyon bayan takarar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, kafin a gudanar da zaben fitar da 'yan takara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel