Sakamakon jibgar jami'in VIO: Kotu ta garkame wani direban babbar mota

Sakamakon jibgar jami'in VIO: Kotu ta garkame wani direban babbar mota

A ranar Juma'a, wata babbar kotun majistire da ke zama a Isabo, Abeaokuta, ta garkame wani direban babbar mota, Nurudeen Bashir a gidan kaso, sakamakon dukan wani jami'in hukumar binciken motoci (VIO), a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Ana tuhumar Bashir da jiwa wani mai tuka mashin ciwo, a lokacin da yake kokarin tserewa jami'in hukumar ta VIO.

Jami'a mai shigar da kara, Sifeta Bukky Abolade, ta shaidawa kotun cewa a ranar Laraba, a garin Aro a cikin Abeokuta, jami'in VIO din ya tsayar da wanda ake zargin, inda ya gaza fito da takardun motarsa.

KARANTA WANNAN: Kan shirin TraderMoni: Saraki ya yiwa Osinbajo da APC wankin babban bargo

Sakamakon jibgar jami'in VIO: Kotu ta garkame wani direban babbar mota

Sakamakon jibgar jami'in VIO: Kotu ta garkame wani direban babbar mota
Source: Twitter

Abolade ta bayyana cewa Bashir ya tafi da wani jami'in hukumar wanda ya shiga cikin motarsa har zuwa Oketa-Ata, inda shi da wasu suka yiwa jami'i dukan kawo wuka.

Babban mai shari'a a kotun, Adeola Adelaja, ya bayar da umurni da a garkame wanda ake zargi a kurkuku har sai ranar 14 ga watan Disamba, inda za a iya duba batun bayar da belinsa, tare da ci gaba da sauraron shari'ar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel