Wata sabuwa: Jam'iyyu 75 suna barazanar janye wa daga zaben 2019, ko me yayi zafi?

Wata sabuwa: Jam'iyyu 75 suna barazanar janye wa daga zaben 2019, ko me yayi zafi?

- Kungiyar shuwagabannin jam'iyyun siyasa 75 tayi barazanar fitar da hannun ta daga zaben 2019

-Shuwagabannin sunyi alkawarin aiki tare da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta

- Sabon tsarin zaben zai taka rawar gani gurin tabbatar zabe mai inganci

Wata sabuwa: Jam'iyyu 75 suna barazanar janye wa daga zaben 2019, ko me yayi zafi?

Wata sabuwa: Jam'iyyu 75 suna barazanar janye wa daga zaben 2019, ko me yayi zafi?
Source: UGC

Shuwagabannin jam'iyyun siyasa 75 karkashin inuwar kungiyar shawara tsakanin jam'iyyu a jiya tayi barazanar tsame hannun ta daga zaben 2019 matukar shugaban kasa bai amince da sabbin tsarin zabe da aka gabatar ba.

Shugaban kungiyar, Chief Peter Ameh-led yayi alkawarin aiki tare da shugaban hukumar zabe don tabbatar da anyi ingantaccen zabe.

An yanke shawarar ne a taron da akayi a hukumar zabe mai zaman kanta a Abuja wanda ya samu halartar shuwagabannin jam'iyyun siyasa 75 cikin 91 na kasar nan.

DUBA WANNAN: Auren Priyanka ya lakume N21b

"Kungiya ta yanke shawarar cewa, tunda yan Najeriya na bukatar zabe mai inganci wanda sabon tsarin nan ne kadai zai iya tabbatar da hakan, mu a matsayin mu na masu ruwa da tsaki muna kira ga shugaban kasa da ya hanzarta amincewa don a maida tsarin doka. Idan kuma yaki, toh zamu tsame hannun mu daga duk wata harkar zabe a 2019," inji IPAC.

Kungiyar ta zargi cewa tsaikon ko rashin sa hannu a sabon tsarin zai iya jefa kasar a wani halin rikicin zabe tare da jefa INEC cikin tsaka mai wuyar da zata sa su kasa yin zabe mai inganci.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel