Dalilin da ya sa zaben Atiku zai fi zama alheri ga 'yan Najeriya - Saraki

Dalilin da ya sa zaben Atiku zai fi zama alheri ga 'yan Najeriya - Saraki

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta ce dan takarar shugabancin kasar ta, Atiku Abubakar ya cika ka'idojin da 'yan Najeriya za suyi amfani dashi wajen tattance wanda za su zaba ya shugabanci kasar a zaben 2019.

Shugaban majalisar dattawa kuma Directa Janar na yakin neman zaben shugabancin kasa na PDP, Bukola Saraki ne ya yi wannan jawabin a taron manema labarai da ya kira ranar Juma'a a Abuja.

Mr Saraki ya ce 'yan Najeriya suna bukatar shugaban kasa da ya fahimci tattalin arzikin kasa, wanda zai janyo masu saka hannun jari ya kuma kare dukiyoyi da rayyukan 'yan Najeriya.

Dalilin da ya sa zaben Atiku zai fi zama alheri ga 'yan Najeriya - Saraki

Dalilin da ya sa zaben Atiku zai fi zama alheri ga 'yan Najeriya - Saraki
Source: Twitter

Ya ce jam'iyyar PDP tana da dan takarar da ya fahimci abubuwan da zai aikata domin ciyar da Najeriya gaba, ya janyo masu saka hannun jari sannan ya hada kan 'yan Najeriya kuma ya tafi tare da kowa a gwamnatinsa.

DUBA WANNAN: Goyon bayan Buhari: Wata kungiya ta nemi gwamnan Anambra ya yi murabus

"Munyi imanin cewa Atiku Abubakar yana da kwarewa da fahimta da zai iya magance wadannan matsalolinm," inji Saraki.

Mr Saraki ya kuma jadada cewa za su mayar da hankali ne kan yadda da za su magance matsalolin 'yan Najeriya a yayin yakin neman zabensu.

Ya ce abinda jam'iyyarsu ta sanya a gaba shine yadda za a inganta tattalin arziki da rayuwan talakawan Najeriya.

"Abinda ya fi ci mana tuwa a kwarya a Najeriya shine tattalin arziki, shin za mu iya cewa talakan Najeriya ya samu cigaba?

"Amsar dai itace tattalin arziki, kuma idan ana son habbaka tattalin arziki ya zama dole a zabi shugaban kasa da ya fahimci tattalin arziki ta yadda zai samawa matasa ayyukan yi.

"Idan ana son cimma wannan manufar, bai wai kashe kudade kawai za a rika yi ba, dole gwamnati ta samar da yanayin da masu saka hannu jari za su zo kasar su saka jari," inji Saraki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel