Kan shirin TraderMoni: Saraki ya yiwa Osinbajo da APC wankin babban bargo

Kan shirin TraderMoni: Saraki ya yiwa Osinbajo da APC wankin babban bargo

- Bukola Saraki, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirinta na TraderMoni tunda dai,a cewarsa, ya koma shirin siyasa tsantsa don yada jam'iyyar APC da harkokinta

- Saraki ya kuma kalubalanci yaddagwamnati ke bukatar katin zaben dukkanin wadanda zasu ci gajiyar shirin, wanda a cewarsa hanyar sayen kuri'un jama'a ne

- Ya bayar da shawara kan cewar idan har ana son wannan shirin ya ci gaba da gudana, to kuwa ya zama wajibi a sanya 'yan siyasa daga jam'iyyun hamayya na kasar

Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirinta na TraderMoni tunda dai,a cewarsa, ya koma shirin siyasa tsantsa don yada jam'iyyar APC da harkokinta, mai makon shiri don bunkasa 'yan Nigeria.

Gwamnatin tarayya dai ta yi ikirarin cewa ta bullo da shirin TraderMoni don tallafawa kananan 'yan kasuwa da jarin da zasu bunkasa kasuwancinsu ta hanyar basu rancen N10,000 kowanne.

Saraki ya kuma kalubalanci makasudin bullo da shirin, musamman ganin yadda jami'an gwamnatin tarayyar ke bukatar katin zaben dukkanin wadanda zasu ci gajiyar shirin, wanda a cewarsa wannan alama ce karara da ke nuna cewa an mayar da shirin hanyar sayen kuri'un jama'a.

KARANTA WANNAN: Sakamakon yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta rike albashin malaman jami'a

Kan shirin TraderMoni: Saraki ya yiwa Osinbajo da APC wankin babban bargo

Kan shirin TraderMoni: Saraki ya yiwa Osinbajo da APC wankin babban bargo
Source: Depositphotos

Da yake zantawa da manema labarai a Abuba a ranar Juma'a, babban daraktan kungiyar yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya kuma yi nuni da cewa 'yan siyasar APC ne kadai aka sanya a cikin shirin, wanda hakan ba dai dai bane a cewarsa ma damar dai an bullo da shirin don amfanuwar 'yan Nigeria.

Ya bayar da shawara kan cewar idan har ana son wannan shirin ya ci gaba da gudana, to kuwa ya zama wajibi a sanya 'yan siyasa daga jam'iyyun hamayya na kasar, don dai-daita lamarin da kuma yin adalci ga kowa.

Saraki ya bayyana mamakinsa kan yadda shirin ya zama babban aikin bunkasa jama'a da gwamnatin mai ci a yanzu ke takama da shi wajen cimma muradunta na siyasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel