Sakamakon yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta rike albashin malaman jami'a

Sakamakon yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta rike albashin malaman jami'a

- Gwamnatin tarayya ta umurci shuwagabannin jami'o'in gwamnati da su kakaba tsarin nan na ba aiki ba biyan albashi ga malaman jami'ar da suke yajin aiki

- Wannan sabon umurni ya kuma yi nuni da cewa biyan malaman albashi daga kowacce fuska zai zama kamar kin bin wannan umurni na gwamnati

- Da yake maida martani akan wannan umurni, shugaban kungiyar ASUU reshen jami'ar Ibadan, Dr Deji Omole, ya ce sam umurni ba zai hanasu ci gaba da yajin aikin ba

Gwamnatin tarayya ta umurci shuwagabannin jami'o'in gwamnati da su kakaba tsarin nan na ba aiki ba biyan albashi ga malaman jami'ar da suke yajin aiki.

Wannan umurnin da gwamnatin tarayyar ta baiwa jami'o'in na kunshe ne a cikin wata wasika daga hukumar kula da harkokin jami'o'in gwamnati na kasar zuwa ga shuwagabannin jami'o'i.

Wasikar, wacce daraktan sashen bincike, tattara bayanai da fasaha na hukumar Dr S. B Ramon Yusuf ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa biyan malaman albashi daga kowacce fuska zai zama kamar kin bin wannan umurni na gwamnati.

KARANTA WANNAN: A karon farko: Amurka ta maidawa gwamnatin Buhari martani kan bukatar hana Atiku 'Visa'

Sakamakon yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta rike albashin malaman jami'a

Sakamakon yajin aikin ASUU: Gwamnatin tarayya ta rike albashin malaman jami'a
Source: Depositphotos

Wasikar ta ce: "La'akari da yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'i ke kan yi a fadin kasar, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar cewa babu albashi na kowacce siga, ko alawus alawus ga malaman jami'o'in da ke yajin aiki.

"Haka zalika, gwamnatin tarayya na umurtar dukkanin shuwagabannin jami'o'in gwamnati da su kakaba tsarin nan na ba aiki ba albashi. Haka zalika, jami'o'i su biya ma'aikatan jami'ar da ba malamai ba albashinsu. Sannan shuwagabannin jami'o'in su sani cewa, biyan malaman da ke yajin aiki albashi daga kowacce fuska, alama ce ta bijirewa umurnin gwamnatin tarayyar Nigeria."

Da yake maida martani akan wannan umurni na gwamnatin tarayya, shugaban kungiyar malaman jami'a ASUU reshen jami'ar Ibadan, Dr Deji Omole, ya ce abun kunya ne ace gwamnatin tarayya ta rikewa malaman jami'a albashi da alawus alawus har na shekaru 7 amma har take so suci gaba da aiki, yayin da ita fadar shugaban kasar da majalisun tarayya suke babakere akan dukiyar kasar.

Omole ya yi nuni da cewa wannan sabon umurnin na gwamnatin tarayya ba zai karayar da zuciyarsu ba, illa ma ya kara rura wutar bin diddigin bukatarsu, yana mai cewa mambobin kungiyar ASUU sun cimma matsaya kan baiwa daliban Nigeria ilimi mai inganci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel