Yanzu-yanzu: George Bush ya mutu

Yanzu-yanzu: George Bush ya mutu

An sanar da mutuwar tsohon shugaban kasan Amurka, George HW Bush kuma mahaifin tsohon shugaban kasa George a rana Asabar, 1 ga watan Disamba, 2018.

Bush ya mutu ne bayan uwargidarsa Barbara Bush ta mutu ranan 17 ga watan Afrilu ta nada shekaru 92. Kwanaki kadan bayan mutuwarta, Bush ya fara wani rashin lafiya.

An haifi Bush ne cikin rayuwan siyasa da shugabanci, bayan kasancewanshi dan Sanatan Amurka, direban jirgin yaki a yakin duniya na biyu, shugaban wasan gudu a makaranta, dan majalisan wakilan, ya rike kujeran shugaban jam'iyyar Republican.

Yanzu-yanzu: George Bush ya mutu

Yanzu-yanzu: George Bush ya mutu
Source: Depositphotos

A shekarar 1980, bai samu nasarar takara kujeran shugaban kasa ba, amma ya kasance mataimakin shugaban kasa karkashin tsohon shugaban Amurka, Ronald Reagan, sannan yayi takaran shugaban kasa a 1988 kuma ya samu nasara bayan lallasa Micheal Dukakis na jam'iyyar Democrats.

Bayan shekara hudu a fadar White House, George Bush, ya sake takara kujeran a 1992 amma Bill Clinton na jam'iyyar Democrats ya lallasa shi. Tun daga lokacin, bai sake takarar wata kujera ba har mutuwansa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel