Zan ci gaba da kasancewa a APC don marawa tazarcen Buhari baya – Sanata Marafa

Zan ci gaba da kasancewa a APC don marawa tazarcen Buhari baya – Sanata Marafa

- Sanata Kabiru Marafa ya sha alwashin ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC

- Ya ce zai marawa Shugaba Buhari baya har sai ya cimma burinsa na son tazarce

- Marafa ya kuma ce sai ya ga bayan rashin adalci a jam'iyyar

Bayan rahotanni da ke nuna cewa yan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara na shirin sauya sheka daga jamiyyar, daya daga cikin yan takarar, Sanata Kabiru Marafa ya sha alwashin ci gaba da kasancewa a jam’iyyar.

Marafa, wanda ke wakiltan Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa ya ce zai ci gaba da marawa kudirin tazarcen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya yayinda yake yaki da ganin adalci a jam’iyyar mai mulki.

Zan ci gaba da kasancewa a APC don marawa tazarcen Buhari baya – Sanata Marafa

Zan ci gaba da kasancewa a APC don marawa tazarcen Buhari baya – Sanata Marafa
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa sanatan zai ci gaba da yin biyayya ga jam’iyyar da kuma kokarin ganin nasararta a 2019.

KU KARANTA KUMA: Dan majalisa ya zargi kungiyoyi masu zaman kansu da tallafa wa Boko Haram

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Alhaji Ahmed Lawan ya shawarci jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da matsawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan sanya hannu akan dokar zaben 2019.

Lawan ya bayar da shawarar ne a lokacin da yake amsa tambaya sa ga manema labarai na majalisa a Abuja a ranar Juma’a, 30 ga watan Nuwamba.

Ya yi gargadin cewa shugaban kasar ba zai sanya hannu a dokan zabe batare da nazarin takardun ba don guje ma kura-kurai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel