Goyon bayan Buhari: Wata kungiya ta nemi gwamnan Anambra ya yi murabus

Goyon bayan Buhari: Wata kungiya ta nemi gwamnan Anambra ya yi murabus

- Wani bangare na jam'iyyar APGA ya yi kira da gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya yi murabus

- An nemi gwamnan ya yi murabus ne domin bayyana goyon bayansa ga shugaba Buhari a zaben 2019 duk da cewa jam'iyyarsu tana da dan takarar shugabancin kasa

- Kungiyar ta bayyana cewa abinda gwamnan ya yi cin fuska ne da sabawa kundin tsarin mulkin jam'iyyarsu

Goyon bayan Buhari: Wata kungiya ta nemi gwamnan Anambra ya yi murabus

Goyon bayan Buhari: Wata kungiya ta nemi gwamnan Anambra ya yi murabus
Source: Depositphotos

Wata bangare na jami'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), da ke kiran kansa da suna Authentic All Progressives Grand Alliance (AAPGA) ya bukaci gwamna Willie Obiano na jihar Anambra ya yi murabus daga kujerarsa gwamna da Ciyaman din kwamitin amintattu na APGA saboda ya goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 ba tare da tunttubar shugabanin jam'iyyar ba.

Ciyaman din jam'iyyar na kasa, Cif Jerry Obasi ya shaidawa manema labarai a ranar Juma'a a Abuja cewa gwamnan ya janyo wa jam'iyyar abin kunya wadda hakan yasa yanzu duk masu hankali a Najeriya suke musu dariya.

DUBA WANNAN: Kotu ta soke afuwar da Tambuwal ya yiwa wasu da ake zargi da satar N15bn

Ya koka kan yadda gwamnan ya goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari a wajen taron kaddamar da littafin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan mai suna 'My Transition Hours' duk da cewa jam'iyyar na da dan takarar shugabancin kasa Janar John Gbor mai murabus.

AAPGA ta zargi gwamna Obiano ta yiwa jam'iyyar zagon kasa da sabawa kundin tsarin mulkin jam'iyyar sashi na 22(2D) wadda tuni sun mikawa hukumar zabe mai zaman kanta INEC.

Obasi ya ce jam'iyyar ta kauce hanya daga ainihin akidun da aka kafa ta kai wadda shi ke sanya talakawa rungumar jam'iyyar.

"Akwai bukatar 'yan jam'iyya na ainihi masu biyaya su bullo da wata shirin domin dawo da martabar jam'iyyar da akidun da aka kafa ta a kai. Wannan shirin zai hada da sulhu da hadin kai dukkan wadanda su kayi gwagwarmaya domin ganin APGA ta cimma burinta na ceto talakawa daga kangin da suka shiga," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel