Jam'iyyu 73 za su fafata takarar shugaban kasa a zaben 2019 - INEC

Jam'iyyu 73 za su fafata takarar shugaban kasa a zaben 2019 - INEC

A juma'a da wasu Hausawan ke kiranta Jumma'au Babbar rana, Hukumar zabe ta kasa watau INEC ta bayyana cewa, a halin yanzu jam'iyyu 73 ne kacal ke hankoron kujerar shugaban kasa da za su fafata a yayin babban zabe na 2019.

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, hukumar ta bayyana cewa a halin yanu jam'iyyu 73 sun fidda 'yan takarkarin su na kujerar shugaban kasa yayin da a yau wa'adin hukumar ya ciki na sauya dan takara ko janyewa.

Shugaban hukumar zaben na kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu, shine ya zayyana hakan yayin bikin bude wani taron karawa juna sani da aka gudanar na kwanaki biyu tare da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Jam'iyyu 73 za su fafata takarar shugaban kasa a zaben 2019 - INEC

Jam'iyyu 73 za su fafata takarar shugaban kasa a zaben 2019 - INEC
Source: Depositphotos

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, hukumar zabe gabanin wannan rahoto ta bayar da sanarwar 'yan takara na jam'iyyu 79 da ke hankoron kujerar shugaban kasa a yayin babban zaben kasa na badi.

KARANTA KUMA: Rai 1 ya salwanta, Mutane 7 sun jikkata a wani sabon Harin Boko Haram kan Dakarun Sojin Kasa

Farfesa Yakubu ya kara da cewa, hukumar nan ba da jimawa ba za ta wallafa sunayen 'yan takarar kujerar ta shugaban kasa tare da jam'iyyun su a bisa tafarki da kuma tsare-tsare da hukumar ta shimfida cikin jadawalin ta.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya a ranar Asabar 16 ga watan Fabrairun 2019 yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da kuma na majalisun dokoki na jihohi a ranar Asabar 2 ga watan Maris.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel