Shehu Sani ya caccaki kiran da gwamnatin tarayya ta yi akan bizan Atiku

Shehu Sani ya caccaki kiran da gwamnatin tarayya ta yi akan bizan Atiku

Dan majalisa mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan kasar, Shehu Sani ya yi watsi da kiran da gwamnatin tarayya ta yi wa kasar ASmurka kan batun ba dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar biza.

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnatin tarayya ta fada ma kasar Amurka cewa ta hankalta wajen ba Atiku biza don kada hakan ya sa a ga kamar ta marawa tsohon mataimakin shugaban kasar baya a zaben 2019.

Shehu Sani ya caccaki kiran da gwamnatin tarayya ta yi akan bizan Atiku

Shehu Sani ya caccaki kiran da gwamnatin tarayya ta yi akan bizan Atiku
Source: Depositphotos

Dan majalisan wanda yayi martani ga kiran gwamnatin tarayyan a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 30 ga watan Nuwamba yace shawarar bai dace baa bun Allah wadai ne.

KU KARANTA KUMA: Da ni da Bishop Crowther daya mu ke, daga tsatson annabi Ibrahim mu ka fito - Buhari

Ya rubuta a twitter: “Fada ma wata kasa a waje cewar kada ta ba dan kasarka biza kan hujjar cewa dan takara ne; kuma ba tare da hujjar aikata laifi ba ko take dokar kasa bai kamata ba kuma abun Allah wadai ne."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel