A karon farko: Amurka ta maidawa gwamnatin Buhari martani kan bukatar hana Atiku 'Visa'

A karon farko: Amurka ta maidawa gwamnatin Buhari martani kan bukatar hana Atiku 'Visa'

- Amurka ta ce batu kan baiwa 'yan Nigeria takardar shiga kasar Amurka walau mai matsayi ko maras matsayi wani babban lamari ne kuma boyayye

- Hakan martani ne kan cece-kucen da ya mamaye kasar na sanin matsayar takardar izinin Atiku Abubakar, ta shiga kasar Amurka

- Amurka ta ce bayanan takardar na sirri ne a wajen gwamnatin kasar Amurka, kuma babu wanda zai taba bayyana bayanan ga kowa, koda kuwa shugaban kasa ne

A ranar Juma'a, jami'in hulda da jama'a na ofishin jakadancin kasar Amurka da ke Legas, Mr. Brussel Brooks, ya ce batu kan baiwa 'yan Nigeria takardar shiga kasar Amurka walau mai matsayi ko maras matsayi wani babban lamari ne kuma boyayye.

Ya ce gwamnatin Amurka ba zata tattauna irin wannan batu da kowa ba.

Brooks ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan kammala wani taro kan Ilimi, da aka gudanar a cibiyar karatun nesa da ke jami'ar Ibadan.

Jami'in hulda da jama'ar yana maida martani ne kan cece-kucen da ya mamaye kasar na sanin matsayar takardar izinin mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, kuma dan takatrar shugaban kasakarkashin jam'iyyar PDP, ta shiga kasar Amurka.

KARANTA WANNAN: Kan zaman lafiya: Buhari ya yiwa 'yan Nigeria wa'azi, ya kafa hujjoji daga ayoyin Injila

A karon farko: Amurka ta maidawa gwamnatin Buhari martani kan bukatar hana Atiku 'Visa'

A karon farko: Amurka ta maidawa gwamnatin Buhari martani kan bukatar hana Atiku 'Visa'
Source: Depositphotos

A cewar Brooks, batu kan matsayar takardar izin Atiku na shiga kasar Amurka ya dade a hannun mahukuntan kasar Amurka, "Sai dai kamar kowanne lokaci, ire iren wannan batutuwa na da girman gaske kuma boyayyu ne.

"Bama tattauna ire iren wadannan batutuwa da suka shafi takardar Visa da kowanne mutumi, komai matsayinsa a gwamnatance ko a hukumance, walau shugaban kasa ko jama'ar gari.

"Duk wanda zai cike bukatar samun takardar izini ya sani cewa akwai wasu muhimman bayanai da ake ajiyewa. Wannan takardar kuwa tana ta sirri ce a wajen gwamnatin kasar Amurka, kuma babu wanda zai taba bayyana bayanan da ke ciki ga gama gari."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel