Sanatoci za su tattauna game da batun gina Jami’o’i a Najeriya

Sanatoci za su tattauna game da batun gina Jami’o’i a Najeriya

- Sanatoci sun dage zaman Majalisa jiya saboda taron Jam’iyyar PDP

- Shugabannin Majalisar Dattawa ba su bayyana dalilin daga zaman ba

- ‘Yan Majalisar sun kuma amince a gina wata Makaranta a Katsina

Sanatoci za su tattauna game da batun gina Jami’o’i a Najeriya

Bukola Saraki ya dage zaman Majalisar Dattawa saboda taron PDP
Source: Depositphotos

Mun samu labari daga Hukumar dillacin labarai na NAN cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta dage zaman da ta shirya jiya Alhamis saboda babban taron da aka shirya na Jam’iyyar PDP a Hedikwatar Jam’iyyar adawar.

Zaman Majalisar da aka yi jiya bai wuce sa’a guda ba inda aka tattara aka tafi taron Majalisar NEC na Jam’iyyar PDP. Sanatocin Kasar ba su tattauna game da batun da ke gaban su ba, sai aka tattara aka rufe Majalisar Tarayyar.

KU KARANTA: Kwamitin yakin neman zaben Atiku ta nada Melaye a matsayin Kakaki

A ka’ida dai Sanatocin ba su yi maganar kokarin kashe Sanata Dino Melaye da aka yi ba. Haka kuma Majalisar tayi watsi da batun da su ka shafi gidajen yarin Kasar. Yanzu dai Sanatocin ba za su zauna ba sai a makon gobe.

Sanatocin sun tashi ne bayan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya dage zaman. Jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kaddamar da kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar da Peter Obi mai dauke da mutane har 154.

‘Yan Majalisar sun amince a gina wata Makarantar gaba da Sakandare a Garin Daura a cikin Jihar Katsina. Hakan na zuwa ne bayan wani aiki da kwamitin da ke kula da Hukumar TETFund tayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel