2019: A tabbatar da Zabe na gaskiya da adalci - Sarkin Musulmi ya gargadi Gwamnatin Tarayya

2019: A tabbatar da Zabe na gaskiya da adalci - Sarkin Musulmi ya gargadi Gwamnatin Tarayya

Za ku ji cewa Sarkin Musulmi watau Sultan na Sakkwato, Alhaji Sa'ad Abubakar na III, ya gargadi gwamnatin tarayya karkashin jagoranci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan tabbatar da gaskiya gami da adalci yayin babban zabe na 2019.

2019: A tabbatar da Zabe na gaskiya da adalci - Sarkin Musulmi ya gargadi Gwamnatin Tarayya

2019: A tabbatar da Zabe na gaskiya da adalci - Sarkin Musulmi ya gargadi Gwamnatin Tarayya
Source: Depositphotos

Sultan na Sakkwato wanda Sarkin Keffi, Dakta Shehu Chindo Yamasu ya wakilta, ya yi wannan kira ne a yau Juma'a yayin halartar taron Cibiyar Musulmai ta Mata karo na 29 da aka gudanar a babban birnin kasar nan na tarayya.

Dakta Shehu ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan wanzar da tsantsar gaskiya gami da adalci yayin zaben 2019 domin tabbatar da da'a ga sashe na 31 cikin kundin tsari da manufa ta majalisar dinkin duniya akan kare martaba da hakkin dan Adam.

Sarkin Musulmin ya bayyana cewa, "tabbatar da cikar burin kowace al'umma na da nasaba ga tsare-tsare da hukunce-hukunce na kowace gwamnatin da ke jagorantar su."

KARANTA KUMA: Ina adawa da Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea - Tinubu

A sanadiyar haka Sarkin na Musulmi ya yi kirayi ga wannan kungiya kan tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya daidai gwargwado da karfin ikon ta tare da goyon bayan cibiyoyi da kungiyoyin Musulmi wajen cimma manufar ingataccen zabe.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya Alhamis shugaban kasa Buhari ya ziyarci fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar El-Kanemi, yayin ziyarar jajantawa dakarun soji dangane da tsautsayi na harin mayakan Boko Haram da ya afka ma su makonni kadan da suka shude.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel