Har yanzu shugaba Buhari ya kasa cire Shittu bayan bayyi bautar kasa ba

Har yanzu shugaba Buhari ya kasa cire Shittu bayan bayyi bautar kasa ba

- Har yau ministan yada labarai na nan daram a kujerar shi

- Watanni biyu da kwanaki goma da jaridar Premium Times ta fallasa rashin takardar shaidar hidimar kasar shi

- Mista Shittu da kanshi ya tabbatarwa da PREMIUM TIMES cewa bai yi hidimar kasa ba

Har yanzu shugaba Buhari ya kasa cire Shittu bayan bayyi bautar kasa ba

Har yanzu shugaba Buhari ya kasa cire Shittu bayan bayyi bautar kasa ba
Source: Facebook

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi shiru har yanzu akan maganar ministan yada labarai, Adebayo Shittu.

Watanni biyu da kwanaki goma kenan da jaridar Premium Times ta fallasa rashin takardar shaidar hidimar kasar shi.

Wata ministan ma'aikatar kudi wacce makamancin hakan ya faru da ita, ajiye aiki tayi.

Amma a na Mista Shittu, gwamnati bata dau wani mataki ba duk da ministan ya karbi laifin shi.

Jam'iyyar APC a watan Octoba ta hana Mista Shittu tsayawa takarar gwamnan jihar shi ta Oyo saboda tsallake wajibin hidimar kasa da baiyi ba.

DUBA WANNAN: Dalla-dalla: Yadda aka fanso tagwayen Zamfara

Jam'iyyar amma har yanzu ba tayi wani yunkurin sauke shi daga matsayin shi ba.

Mista Shittu dai ya kammala karatun shi na matakin digiri a jami'ar Ife, yanzu Obafemi Awolowo University, Ile Ife a lokacin yana da shekaru 25. Yakamata ace Shittu yayi wajitacciyar hidimar kasa ta shekara daya amma yaki.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel