Yanzu-yanzu: Rundunar soji sun kaiwa yan Boko Haram mumunan farmaki

Yanzu-yanzu: Rundunar soji sun kaiwa yan Boko Haram mumunan farmaki

Hukumar sojin Najeriya ta samu wani gagarumin nasara kan yan tada kayar bayan Boko Haram a ranan Alhamis, 29 ga watan Nuwamba, 2018 a gadan Ngala da Gamboru a jihar Borno.

Dakarun sojin sun kai wannan hari ne bayan umurnin babban hafsan sojin Najeriya ya bada umurnin cigaba da kai hari sansanin yan Boko Haram.

Yanzu-yanzu: Rundunar soji sun kaiwa yan Boko Haram mumunan farmaki

Yanzu-yanzu: Rundunar soji sun kaiwa yan Boko Haram mumunan farmaki
Source: Facebook

KU KARANTA: Buratai ya bada odan bincike kan sansanin horar da yan bindigan da aka gano a jihar Ribas

Tukur Buratai ya bayyana sabanin umurnin da ya bada a baya cewa a daina neman yan Boko Haram cikin daji, innama a saurari zuwansu sannan a hallaka su, yanzu a durfafesu duk inda suke.

Hukumar ta saki wannan jawabi ne da yammacin Juma’a, 30 ga watan Nuwamba, 2018.

Yanzu-yanzu: Rundunar soji sun kaiwa yan Boko Haram mumunan farmaki

Yanzu-yanzu: Rundunar soji sun kaiwa yan Boko Haram mumunan farmaki
Source: Facebook

Jawabin yace: “Bisa ga umurnin COAS Lt Gen TY Buratai cewa kwamandojin rundunar OP LAFIYA DOLE su durfafi mabuyar Boko Haram da kai musu hari, jami’an 3 Battalion Ngala sun kai mumunar hari ranan 29 ga watan Nuwamba, 2018.”

"Jami’an sun kai harin kwantan baunan ne ta fuska biyu. Ta gadan Ngala da Gamboru, sannan kauyen Wurge duk a jihar Borno.

An kwato manyan makai, mota 1, mashian 2, da daruruwan harsasai."

A bangare guda, Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusufu Buratai, ya bada umurnin gudanar da bincike mai zurfi cikin sansanin horar da yan bindigan da aka gano a karamar hukumar Tai a jihar Ribas.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel